An tambayi wani Mai Hikima "Shin wacece Mafi alkhairi acikin Mata?? (Wato Mace tagari) Sai yace:
1. Ita ce mai kokarin neman yardar Ubangijinta. Ta hanyar sauke wajibabbun hakkokin dake kanta.
2. Mai shiryar da Mijinta (idan ya 'bata). Kuma tana Taimaka masa wajen bin Allah da Manzonsa da Iyayensa da sadar da zumuncinsa.
3. Bata barin gidanta (don yaji, ko kuma yawon banza. Sai dai babban uzuri idan ya kama).
4. Ita ce mai tsananin kulawa da sallolinta biyar (Tana yinsu akan lokaci, kuma tare da tsoron Allah).
5. Ita ce mai 'boye sirrinta da sirrin Mijinta (Ko sun 'bata da Miji ko abokiyar zama, babu wanda zai sani).
6. Ba'a ganin takalminta ko Kayan adonta idan tana tafiya (wato ta rufe jikinta baki daya).
7. Ba'a jin sautin muryarta ako ina.
8. Ba'a sanin kamannin siffar Jikinta (Ko yaushe tana sanye da tufafi kammalallu).
9. Abar girmamawa ce acikin Mutanenta, (saboda karamcinta da kyawun halayenta).
10. Mai kaskantar da kai ne acikin zuciyarta. (Bata ganin cewa ita tafi Qarfin kowa)
11. Mai tausayi ce ga 'ya'yanta, kuma tana kulawa da ciyar dasu da shayar dasu.
12. Gidanta tamkar wata Aljannah ce makusanciya (saboda soyayya da sakin fuska da wadatuwar Zuci).
13. Idan ta samu abin alkhairi daga Maigidanta sai ta gode masa afili da boye (Ko yaushe tana yi masa addu'a)
14. Idan ta riski wanni sharri daga gareshi, Takan yi hakuri. (Ba wai tayi masa masifa ko haya-gaga ba).
15. Idan ya shigo gareta sai tayi farin ciki ta tareshi da murmushi. (Bata Qullatar kowa azuciyarta)
16. Idan ya fito daga gidanta (zai tafi wajen aiki) zata nuna damuwarta, kuma tana 'dokin dawowarsa.
17. Idan yana fushi da ita takan yi hakuri ta jure, har sai ta bashi hakuri ya huce.
18. Ko yaushe idan ta matso gareshi sai ta burgeshi (saboda kyawun ado da tsafta da kyawawan kalamai).
19. Idan ba ya nan, takan kiyaye masa amanar jikinta (ita kanta) da sirrinsa da gidansa, da dukiyarsa.
20. Idan taga wani laifinsa sai ta boye, ta suturceshi.
21. Idan ya gaya mata uzurinsa, takan karba ta yafe masa.
22. Mai tsananin Kunyar Allah ne da bayinsa. Hatta Maigidanta tana jin nauyinsa.
23. Mai gaskiya ce da rikon amana. (Bata yin Qarya don burge wani, ko kuma don tada husuma)
24. Mai girmama iyayen Mijinta ne da danginsa. (Bata raina iyayen Miji, ko wulakanta 'yan uwansa).
25. Mai rufa asirin Mijinta ce yayin da talauci ya sameshi (takan taimaka masa idan tana da iko).
26. Bata yi masa gori ko habaici ko cin fuska.
27. Ta runtse idanunta da Zuciyarta. Bata kallon kowanne Namiji sai Mijinta, kuma bata tunanin kowanne Namiji sai shi.
28. Tana kwantar da hankalin Maigidanta duk lokacin da yake cikin wani yanayi. Bata zame masa baya. (Koda an bata masa rai akasuwa ko awajen aiki).
29. Tana nuna ma 'Ya'yanta da danginta yadda zasu ga Mutuncin mahaifinsu. Tana kula da tarbiyyarsu.
ZAUREN FIQHU : Ya Allah ka azurta daliban Zauren Fiqhu da irin wadannan matayen, duk wanda ya karanta wannan rubutun kuma yayi farin ciki dashi, shima ka azurtashi da irin wadannan matayen.
Dalibanmu mata kuma, Ya Allah ka azurtasu da irin wadannan halayen, kasa su zama mataye nagari awajen Mazajensu.
Title :
Wacece Mace Ta Gari
Description : An tambayi wani Mai Hikima "Shin wacece Mafi alkhairi acikin Mata?? (Wato Mace tagari) Sai yace: 1. Ita ce mai kokarin neman yardar Ub...
Rating :
5