Tawagar matasa 'yan kasa da shekara 17 ta Nigeria ta doke ta Brazil da ci 3-0 a wasan daf da na kusa da karshe a gasar cin kofin matasa 'yan kasa da shekara 17 ta duniya.
Nigeria ta fara cin kwallo a minti na 29 da fara wasa ta hannun Victor Osimhen kuma minti daya tsakani Kingsley Michael ya kara ta biyu, sannan Udochukwu Anumudu ya ci ta uku a minti na 34.
Nigeria mai rike da kofin matasan wacce ta dauka sau hudu jumulla za ta buga wasan daf da karshe da wacce ta yi nasara tsakanin Ecuador da Mexico a ranar Alhamis.
A ranar Litinin ce za a ci gaba da buga wasannin daf da na kusa da karshe tsakanin Ecuador da Mexico da kuma fafatawa tsakanin Belgium da Costa Rica
Title :
[Video] Nigeria ta doke Brazil 3-0
Description : Tawagar matasa 'yan kasa da shekara 17 ta Nigeria ta doke ta Brazil da ci 3-0 a wasan daf da na kusa da karshe a gasar cin kofin matas...
Rating :
5