Rahotanni sun nuna cewa United Nations Children’s Fund (UNICEF) zata tallafa ma dalibai mata sama da Miliyan 1 a tsarin taimakon ta na 3.
Jaridar Leadership ta bayyana cewa, wakilin UNICEF na jihar Kaduna, Mr Utpal Moistra me ya bayyana haka a ranar Talata 3 ga watan Nuwamba, a Minna a jihar Nija.
Yace: “Bari in kara bayyana maku, aikin GEP na shirin kara dalibai mata Miliyan 1 a jihohi GEP guda 5 na, Nija, Katsina, Kaduna, Zamfara da Bauchi.
“Zamuyi haka ne domin tallafa ma matan da kuma basu dama.”
Wakilin kuma yayi Kira ga Gwamnatin Jihar Nija data sanya kudade da yawa domin tabbatar da cigaba Ilimin ya’ya Mata.
Title :
UNICEF Zata Tallafa Ma Dalibai Mata Miliyan Daya
Description : Rahotanni sun nuna cewa United Nations Children’s Fund (UNICEF) zata tallafa ma dalibai mata sama da Miliyan 1 a tsarin taimakon ta na 3. J...
Rating :
5