Manzon Allah (saww) ya kasance idan zai mike tsaye yana mikewa ne gaba dayansa. Kuma idan zai tafiyarsa yana yi ne cikin sauri tare da nutsuwa.
Yana tafiya Sahabbansa na gefensa. Domin shi ba'a yin tafiya daf da bayansa Saboda Mala'ikun dake tare dashi. Sahabbansa sai dai su tsaya agefensa, ko kuma su bari idan ya tafi su bishi abaya.
Abu Hurairah (ra) yace "Mun kasance muna binsa aguje alhali shi kuwa yana tafe acikin nutsuwarsa (saww)".
Idan yana tafiya yana cirawa ne dukkansa. Kuma shi yana ganin bayansa kamar yadda yake ganin gabansa. Don haka ba ya waiwaye. Idan zai juya, yana juyawa ne dukkansa (saww).
Idan yana tafiya akan hanya ba'a ganin takun Qafarsa, amma idan yabi ta kan dutse, anan ne alamar takun Qafarsa ke fitowa abayyane (saww).
Wani lokacin idan za'a tafi Jihadi yakan sanya Sahabbansa suyi gaba sannan shi yana biye dasu abaya yana kula da yanayin tafiyar kowa (saww).
Hakika Qurewar daukaka ta tabbata ga Annabin da Qafarsa ta taka har cikin wuta. Ya leka ya zagaya yaga dukkan abinda ke cikinta. Sannan ya leka cikin Aljannah ya shiga cikinta ya zagaya yaga ni'imominta da Qoramunta, da gidajen cikinta.
Qurewar isa da Qasaita ta tabbata ga Annabin da ya taka saman Al'arshi da takalminsa alokacin da yaje Mi'iraji (saww).
Ya Allah kayi salati da tasleemi da albarka bisa Annabina, Macecina, tare da iyalan gidansa tsarkaka kamar yadda kayi Salati da tasleemi da albarka ga Annabinka Ibraheem tare da iyalan gidansa. Hakika kai abin godiya ne, abin Jinjin yabo.