Wata mata mai suna Bara’atu, ’yar shekara 40 a duniya, wacce ke zaune a unguwar Gidan dinya a karamar Hukumar Dutse; ta gurfanar da saurayinta dan shekara 20 da haihuwa a gaban kotu saboda ya yi mata ciki ba ta hanyar aure ba.
A yayin da matar take wa kotu korafi, ta ce saurayin nata mai suna Jamilu yayi watsi da ita bayan ya yi mata ciki, har ta haifu bai yi mata komai ba. Don haka ta bukaci alkali da ya nema mata hakkinta na ciyarwa da sahayar da jaririyar da suka samu tare da shi ba ta hanyar aure ba.
A lokacin da yake amsa tambayoyin alkali, Jamilu, wanda dan asalin karamar Hukumar Dutse ne, ya ce gaskiya ne ya sha kwantawa da matar duk da cewar ta grime shi a yawan shekaru kuma shi ne ya yi mata cikin da ake tuhumarsa a kai.
Saboda haka kotun, a karkashin jagorancin Alkali Ibrahim Yahaya Yayari ya umurci da a tura Jamilu Muhammad gidan wakafi na tsawon kwanaki 14, domin sake sauraran shari’arsa. Ita kuma Bara’atu, kasancewar tana dauke da jaririya sabuwar haihuwa kuma lokaci ne na hunturu, alkalin ya umarci ’yan sandan kotu su bayar da ita beli zuwa lokacin da kotu za ta sake zama domin ci gaba da da shari’ar.
Alkalin dai ya dage sauraren karar zuwa makonni biyu masu zuwa. Kotu kuma ta umurci mahaifiyar jaririyar da ta je ta ci gaba da ba jaririyar kulawa har zuwa lokacin da kotun za ta zartar da hukuncin.
Title :
Saurayi ya yi wa tsohuwa ciki ba tare da aure ba
Description : Wata mata mai suna Bara’atu, ’yar shekara 40 a duniya, wacce ke zaune a unguwar Gidan dinya a karamar Hukumar Dutse; ta gurfanar da saurayin...
Rating :
5