A yayin ziyarar da ya kai sansanin ‘yan gudun hijira na Yola da ke jihar Adamawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsinkayi wata karamar yarinya na ta rusa kuka a dai dai lokacin da sauran mutanen wurin ke ta rafka tafi mata na guda saboda jin dadin irin alkawuran da Buhari yayi musu musamman ma na cewa in Allah Ya so damuna mai zuwa zasu noma gonakin su saboda lokacin BOKO HARAMUN ta zama tarihi(kun ji fa ku masu kukan sai wata yayi kwana talatin ake biyan ku bashi)in da take ya umarci a kawo mashi ita don ya ji ta bakin ta kamar haka:-
Buhari :-Me ya sanya ki kuka?
Yarinya:-Baba ina son in bika gidan ka,
Buhari:-Me yasa kike son ki bini gida?
Yarinya :-Saboda an kashe mini mamata da babana,
Buhari :-Hawaye shar-shar.
Jama’a sun Ga hawaye na kwaranya daga idanun shugaba Buhari lokacin da yarinyar ta shaidawa Buhari dalilin kukan ta.Muna rokon Allah Ya kawo mana karshen wannan masifa da ta addabi al’ummar musulmi.
Title :
[Photos] Wata Yarinya Tasa Buhari Kuka A Yola
Description : A yayin ziyarar da ya kai sansanin ‘yan gudun hijira na Yola da ke jihar Adamawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsinkayi wata karamar yar...
Rating :
5