Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Iran a ranar 23 ga watan Nuwamba domin ya halarci taron kasashe masu Gas.
Shugaban kasa ya isa filin jirgin sama na Mehrabad da misalin karfe 7:15 na dare, Wanda yake misalin karfe 4:44 na rana a Najeriya. Mataimakin Shugaban kasar ne, Shari’at Madri ya karbi shi.
Wadanda suka karbi shugaban kasan sun hada da Dacta Ali Magashi, ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama, ministan wuta Babatunde Raji Fashola, ministan Mai Ibe Kachikwu, mai bada shawara akan sha’anin tsaro, Babagana Munguno.
A cewar Mallam Garba Shehu, Buhari da shuwagabanni kasar Qatar, Russia, Algeria, Oman, Venezuela, Netherlands da kuma United Arab Emirates zasu hadu domin sake duba farashin has a duniya.
Title :
Photos: Isar Buhari Iran
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Iran a ranar 23 ga watan Nuwamba domin ya halarci taron kasashe masu Gas. Shugaban kasa ya isa ...
Rating :
5