A yammacin yau Litinin ne aka bude taron kasashe masu arzikin iskar gas GECF karo na ukku a nan birnin Tehran. Taron ya sami halattar shuwagabannin kasashe 9 da Priminiter guda. Shuwagabannin kasashen Iran, Rasha, Venezuela, Iraqi, Bolivia, Equatorial Guinea, Nigeria, Turkmenistan da kuma Priministan kasar Algeria ne suka sami halattar taron. An gudanar da taron farko na kungiyar GECF a kasar Qatar a shekara ta 2011, sannan na biyu a birnin Mosco na kasar Rasha. Kungiyar ta kasashen masu arzikin iskar gas tana da membobi 18 da kuma kasashe masu sanya ido guda 6. Kasashen GECF sun hada da Algeria, Bolivia, Masar, Equeterial Guenea, Iran, Libya, Nigeria, Qatar, Russia, Trinidad and Tobago, Hadaddiyar daular larabawa. Da kuma Venezuela. Kasashe 6 masu sanya ido kuma sun hada da Kazakhstan, Iraq, Netherlands, Norway, Oman da kuma Peru. Kasar Iran ce a ta ke da arzikin iskar gas mafi yawa a duniya da litre trilliyon 33 a karkashin kasa, kuma a halin yanzu tana hakar litta billion 173 a ko wace shekara, amma tana amfani da mafi yawansa a cikin gida.
Title :
Photos: Buhari Ya Halarci Taron Kasashen Masu Arzikin Iskar Gas A Iran
Description : A yammacin yau Litinin ne aka bude taron kasashe masu arzikin iskar gas GECF karo na ukku a nan birnin Tehran. Taron ya sami halattar shuwag...
Rating :
5