Tsohon shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya kai ziyarar ba-zata zuwa fadar shugaban kasa, inda ya yi tattaunawar sirri da Shugaba Muhammadu Buhari.
Shugabannin biyu sun yi ganawa ta tsawon mintuna goma a fadar Aso Rock kafin Mr Jonathan ya fice a cikin motarsa da ta kai shi.
Tsohon shugaban kasar bai yi wa 'yan jarida bayani ba a kan ziyarar kuma kawo yanzu fadar shugaban kasar ba ta fitar da sanarwa ba a kan ziyarar.
Wannan ce ziyara ta biyu da Mr Jonathan ya kai a fadar Aso Rock tun bayan da ya sauka daga mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
A karshen watan Maris ne shugaba Buhari ya doke Mr Jonathan a zaben shugaban kasar da aka bayyana a matsayin wanda aka gudanar cikin zaman lafiya.
Title :
[Photos] Buhari Ya Gana Da Goodluck Jonathan
Description : Tsohon shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya kai ziyarar ba-zata zuwa fadar shugaban kasa, inda ya yi tattaunawar sirri da Shugaba Muhammad...
Rating :
5