A ranar Laraban nan ne ake sa ran Paparoma Francis zai isa kasar Kenya, a ziyararsa ta farko zuwa nahiyar Afrika.
Kasar Kenya dai na da mabiya darikar Katolika da dama wadanda suka sadaukar da rayuwarsu ga koyarwar cocin ta Katolika.
Yanzu haka wasu 'yan kasar Kenya sun kasa daukar matsaya akan wasu batutuwa da ake ta cece kuce a kan su da suka hada da amfani da magungunan hana daukar ciki na zamani.
Cocin dai tana matukar adawa da batun shan magungunan amma kuma wasu kungiyoyin farar hula suna shelar yin amfani da su.
A na dai zaton cewa ziyarar ta Paparoma ka iya chanja al'amura a kasar.
Title :
Paparoma zai je Kenya
Description : A ranar Laraban nan ne ake sa ran Paparoma Francis zai isa kasar Kenya, a ziyararsa ta farko zuwa nahiyar Afrika. Kasar Kenya dai na da mab...
Rating :
5