Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi, ta caccaki matan da ke amfani da man shafawa domin sa fatar jikinsu ta yi haske, wato bilicin.
Jarumar, wacce ta yi sukar a shafinta na Instagram, ta ce bai kamata mata su rika yin amfani da man shafawar ba domin kawai su burge maza, tana mai cewa hakan kaskantar da kai ne.
A cewar ta, "Na ki yin amfani da man da ke sa fata ta yi haske ne saboda na gamsu da yadda Allah ya halicce ni. Ina murna kan hakan. Allah ya san dalilin da ya yi ni haka, don haka ba zan sauya launin fatata ba".
Nafisa ta kara da cewa, "Wasu matan suna tunanin idan mace ba fara ba ce namiji ba ya sonta, sai su yi ta wahalar da kansu wai sai sun koma farare. Hakan bai dace ba."
Ta kara da cewa mazan da matan ke son burgewa ba sa mayar da hankali a kansu, tana mai cewa, hasalima, mazan ne za su rika aibata matan da ke shafa man da ke haskaka fatarsu.
Wani bincike ya nuna cewa matan da ke yin amfani da man bilicin -- musamman a nahiyar Afirka -- suna matukar karuwa.
Kazalika, binciken ya gano cewa yawan amfani da man da ke kara hasken fata ka iya haifar da cutar sankara (cancer).
Ga Status din da tayi ashafin ta na Instagram
Title :
Nafisah Abdullahi Tayi Allah Wadai Da Matan Da Ke Yin Bilicin
Description : Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi, ta caccaki matan da ke amfani da man shafawa domin sa fatar jikinsu ta yi haske, wato...
Rating :
5