Wadanda suka mutu sun hada da Mata da kananan yara da suka fito daga Dikwa saboda rikicin Boko Haram zuwa garin Maiduguri.
Wani dan kato da gora da ke kula da sansanin ‘Yan gudun hijirar ya shaidawa RFI Hausa cewa matar ta tayar da bom din ne a lokacin da suke tantance mutane a kofar shiga sansanin ‘Yan gudun hijira.
A cewar shi suna cikin tantance Mata ne ‘Yar kunar bakin waken ta zame ta tayar da bom din da ke jikinta.
Akalla mutane 8 suka mutu, bakwai kuma suka jikkata sakamakon harin.
Title :
Mutane 8 sun mutu a harin Maiduguri
Description : Wadanda suka mutu sun hada da Mata da kananan yara da suka fito daga Dikwa saboda rikicin Boko Haram zuwa garin Maiduguri. Wani dan kato da...
Rating :
5