Kimanin mutane 75 suka rasa rayukan su a kasar Mozambique bayan da suka sha wata giya. Jami’an Lafiya na kasar sun bayyana aukuwar wanna lamari a ranar Laraba 4 ga watan Nuwamba. Sun bayyana cewa hakan ya faru ne a yankin Tete na kasar.
Da fari an fara zargin cewa guba aka sanya masu, amma bincike ya nuna cewa babu guba a ciki.
Xinhua news ya bayyana cewa giyar mai suna Pompe bata da wata guba a cikin ta. Sun bayyana cewa gwaji daga kasar Amurka ne ya tabbatar da haka bayan da Afirika ta kudu ta kasa.
Wasu na ganin cewa Fulawa marar kyau ce ta jaza mutuwar mutanen. Yan sanda dai sun saki mai shaida giyar bayan da bincike ya nuna cewa ba’a sanya guba a cikin giyar ba.