A yau ma kamar kullum na samu sakon wata baiwar Allah daga Jami'ar Legas.
A yau maganarmu za ta yi tsokaci ne a kan irin mummunar shigar tsiraici da’yan uwanmu mata suke yi.
Wannan maudu’i na yau
kamar amsa ce game da
tambaya da rokon da wata ’yar uwa daga Jami’ar Legas ta yi cewa don Allah tana rokon a yi fadakarwa a kan wannan maudu’i. Ina rokon Allah Ya shiryar da mu baki daya, Amin.
Ya ku Musulmi! Lallai yana daga cikin Abubuwan da makiyanmu suka yake mu da shi kuma suka ci nasara a kanmu a wannan zamani, shi ne kwararowar wasu irin tufafi, da wasu nau’ukan dinke-dinke marasa kan gado da suka yadu cikin al’ummar Musulmi.
Wadannan tufafi ba sa suturce al’aura saboda gajartarsu, kuma wasu shara–shara ne ko masu matse jiki. Irin wadannan tufafi a
Musulunci harum ne mace ta
sanya su, koda a gaban mata ’yan uwanta ko gaban muharramanta, bare kuma wasu wadanda ba su ba.
Lallai mu sani yana daga alamomin kusantowar Alkiyama, bayyanar shigar tsiraici, ta hanyar sanya matsatstsun tufafi masu bayyana surar jikin mace, ko tufafi masu shara-shara, ko masu wani irin tsagu, ko wani irin tufafi ko dinki da zai kasance kirjin mace da bayanta duk a fili ko cinyoyinta ko kafafuwanta ko wani sassa na jikinta. (Za a ci gaba In Sha Allah).
Allah yasa idan an karanta ai amfani da abin da aka karanta. Ameen
Dan Allah 'yan uwa duk wanda yaga wannan sako ya aikawa yan uwa Musulmi ta hanyar share da COMMENT, LIKE da kuma SHARE don mu samu ladan tunatarwa baki daya.
Title :
Mummunar Shiga Mai Bayyana Tsaraici Da Yan Uwa Mata Ke Yi
Description : A yau ma kamar kullum na samu sakon wata baiwar Allah daga Jami'ar Legas. A yau maganarmu za ta yi tsokaci ne a kan irin mummunar shiga...
Rating :
5