Wani magidanci mai suna Malam Saleh Magaji Baban Salim ya yi wa ’ya’yansa hudu yankan rago a gidansa da ke layin Bello, Unguwar Kawo Kaduna saboda karayar arziki da Allah Ya jarrabce shi da ita.
Lamarin, wanda ya yi matukar tayar wa da mutanen unguwar hankali, inda suka yi ta rusa kuka saboda tausayi a lokacin da ake kwaso gawarwakin yaran cikin jini, ya auku ne a ranar Larabar nan da ta wuce da misalin karfi biyu na rana.
Shi ma maihafin yaran wanda ya yi kokarin kashe kansa ta hanyar yanka makogwaronsa bayan ya halaka yaran nasa, an kai shi asibiti.
Bayanai daga yankin sun ce magidancin yana da ’ya’ya shida ne da mace daya amma ya halaka hudu, biyu suka tsira. Wadanda suka tsira, dayar tana makaranta ne, shi kuma babban mai suna Salim an ce ba ya gidan a lokacin da abin ya faru.
Ita ma mahaifiyar ta su ba ta gidan, domin sun sami sabani da mijin a daren Larabar, inda aka ce ya yi mata dukan tsiya. A cewar wani makwabcinsa, wanda bai ambaci sunansa ba, ya ce yana daya daga cikin wadanda suka kira ’yan sanda bayan an sami labarin cewa an gan shi da wuka a hannunsa bayan matar tasa ta bar gida.
“Ina cikin wadanda suka fara shiga cikin dakinsa bayan ’yan sanda sun iso gidan. Da muka shiga shi muka fara gani a kwance cikin jini sannan da muka shiga cikin uwar daka sai muka tarar da yarinyarsa ’yar shekara daya da wata uku a kwance a kan gado wuyanta a yanke.
“Ganin haka ne sai mutanen da muke tare da su suka fara ficewa, suna kuka saboda takaici. Domin abin ya yi matukar tayar mana da hankali baki dayanmu.
“Gaskiya abin ya ba mu mamaki matuka, domin ban taba tsammanin zai aikata ta’asar ba. A ce wai har zai dauki wuka ya yanka ya’yansa hudu sannan shi ma ya nemi kashe kansa ta hanyar yi wa kansa yankan rago.
“Lamarin babu kyan gani domin ko’ina cikin dakin jini ne a kwance. Tare da shi muke Sallah a masallaci kusan kullum kuma ban taba tunanin zai aikata haka ba. Duk kuwa da mun san cewa ya dan samu jarabawar karayar arziki.” Inji makwabcin nasa, cikin hawaye.
Da Aminiya ta ziyarce gidan da abin ya faru, ta samu jami’an tsaro sun rigaya sun kwashe gawarwakin yaran tare da kai shi mahaifin nasu wanda aka ce bai rigaya ya rasu ba zuwa asibiti. Sai dai kofar gidan ya cika da mutane da suka rika tururuwa zuwa kallo, wasu kuma na ta rusa kuka amma daga baya ’yan sanda sun rufe kofar shiga gidan.
An ce ita ma uwar yaran tuni aka kwashe ta zuwa asibiti bayan ta fita hayyacinta a lokacin da ta sami labarin abin da ya faru da ’ya’yanta.
An ba da sunayen yaran da aka halaka kamar haka: Jibiril da Suleiman da Salman sai kuma Khadija, wacce ba ta wuce shekara daya da wata uku ba.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Zubairu Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce tuni aka kai gawarwakin zuwa asibiti, sannan kuma shi mahaifin nasu yana asibiti ana duba lafiyarsa.
Title :
Magidanci ya yi wa ’ya’yansa 4 yankan rago a Kaduna
Description : Wani magidanci mai suna Malam Saleh Magaji Baban Salim ya yi wa ’ya’yansa hudu yankan rago a gidansa da ke layin Bello, Unguwar Kawo Kaduna ...
Rating :
5