A ranar Laraba ne aka yi janaizar magajin garin Kano Alhaji Inuwa wanda ya rasu a Kano.
Marigayin dai na daga yan siyasa na farko a arewacin Nigeria da suka kafa jam'iyyar NPC tare da sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello, tun gabanin samun mulkin kan Nigeria.
Alhaji Inuwa Wada dai ya yi ayyukan gwamnati da dama baya ga koyar wa a makaranatar Middle.
Shi ne kuma wanda ya kawo scout arewacin Nigeria, ya kuma nemi tsayawa takarar shugabancin Nigeria lokacin NRC da SDP a farkon shekarun 1990.
Marigayin ya taba zama mukaddashin farayi ministan Nigeria, a lokacin da Alhaji Abubakar Tafawa Balewa yake hutu.
Alhaji Inuwa Wada ya rasu ya na da shekaru 98 a duniya, ya bar yaya Takwas, biyar maza hudu mata.
Title :
Magajin Garin Kano Ya Rasu
Description : A ranar Laraba ne aka yi janaizar magajin garin Kano Alhaji Inuwa wanda ya rasu a Kano. Marigayin dai na daga yan siyasa na farko a arewaci...
Rating :
5