“TSAFTA ita ce cikon addini”.
“Ba mai shiga aljanna sai mai tsafta”.
Kaɗan ke nan daga cikin gwalagwalan kalmomin Manzon Allah (SAW) da ya yi a kan muhimmancin tsaftar a sha’anin addini.
Bisa la’akari da muhimmancin tsafta a kowane ɓangare na rayuwar ɗan Adam, shi ya sa ma shafin Himma Dai Mata ya karkato da akalarsa ga maganar tsafta a rayuwar ‘ya mace.
Hakan ya ƙunshi tsaftar ita karan kanta a cikin da ‘ya’yanta da kuma mijinta.
Uwargida muddin aka ce yau kin kasance mai sake wajen kula da tsaftar kanki da ta iyalinki, to, fa a gaskiya ba ki cika ‘ya mace ba, kin zama wacce Hausawa ke kira ‘Kucaka’, domin kuwa ‘ya mace da tsafta aka santa, kuma ita ‘ya mace ‘yar kwalliya ce a kodayaushe.
Sai dai kuma a nan ina son uwargida ta fahimci cewa, tsafta daban, kwalliya kuma daban, amma dai suna tafiya ne kafaɗa da kafaɗa.
Uwargida ya kamata a kodayaushe gidanki ya kasance cikin tsafta, wato a share ko’ina da ko’ina, a gyara shimfiɗu, a wawwanke kwanuka da tukwanen da aka yi amfani da su, a gyara kicin a kuma wanke bayi.
Ki sani, tsaftar bayi da kicin abu ne mai matuƙar muhimmanci ga lafiyar iyalinki domin kuwa ba inda ƙwayoyin cuta suka fi yaɗuwa cikin sauri a gidajenmu kamar waɗannan wurare biyu.
Saboda haka uwargida ki tabbatar a kodayaushe kafin ki ɗora girki sai kin share kicin ɗinki, kin fitar da dukkan kwanuka ko tukwanen da ba su da wanki kin wanke su, sannan a daina barin kayan abinci ko kuma abinci da aka dafa a buɗe domin kauce wa ƙwayoyin cuta waɗanda za su iya kawo cututtuka ga iyalinki kamar kwalara da dai sauransu.
Daga nan kuma sai bayi, uwargida ya kamata a ce a kodayaushe kina tsaftace bayinki yadda ƙwayoyin cuta da sauro ba za su sami wajen zama ba. Kar ki bar ruwa ya riƙa kwanciya a ƙasa, a riƙa rufe masai, a kikkife fon yara, sannan a riƙa bari iska na shiga bayin.
Uwargida muddin ba ki gyara bayin gidanki, to, fa ke kanki wata rana sai ya gagare ki shiga saboda wani irin ɗoyi ko wari da za ki riƙa ji da zarar kin tunkari ƙofar bayin. To, ina ga mai gida, ko ‘ya’yanki ko kuma baƙi masu shigowa. Saboda haka ya kamata ki riƙa kiyayewa domin shi kanshi warin nan yana iya haifar da wata cutar ga wanda ya shaƙe shi.
To, uwargida, idan kin gyara gidanki tsaf, ina labarin tsaftar naki jikin? Da zarar kin gama gyara gidanki da safe, to, fa ki nemi ruwa ki yi wanka ki sa tufafinki masu tsafta. Kar ki zama cikin irin matan nan waɗanda suke yini a gida ba sa wanka sai dai idan za su fita unguwa, ko kuma da yamma idan an ga miji ya kusa dawowa. A’a, da kin gama aikinki, to, ki yi wanka ki sa kayanki masu tsafta yadda ke kanki za ki ji daɗin jikinki kuma duk wacce ta shigo gidanki, ko kuma mijinki ya yi saurin dawowa gida ba kamar yadda ya saba ba, za a ganki tsaf-tsaf, bugu da ƙari ma, Ubangijinmu Ya umarce mu da yin tsafta, da kuma kasancewa cikin tsafta a yayin bauta masa.
Wanka da za ki yi da safe ba kuma zai hana ba idan kin gama girki da yamma, kin sake shasshare duk inda ya kamata, ki sake yin wani wankan ki sanya tufafi, ki yi wa mai gida kwalliya, ki feshe jikinki da tufafinki da turare. Kin ga yin hakan ya gusar da duk wani ƙaurin wuta ko zufa da kika yi a yayin girki.
Uwargida, ki riƙa wanke kanki kina kitso a kai-a kai, ki kuma riƙa yanke gashin hammata da na mara domin su ma waɗannan wurare idan ba kya gyarasu, koda kin yi wanka, to, fa sai an riƙa jin wani wari na daban daga jikinki. Ki kuma riƙa yanke farcenki shi ma a kai-a kai saboda kar ƙwayoyin cuta su sami wurin zama ga shi kuma da hannayen ki ke amfani wajen yi wa iyalinki abinci.
Uwargida, kada a ganki tsaf-tsaf da ke sannan kuma ‘ya’yanki duƙun-duƙun ba wanka, kayansu ba wanki ko ma duk sun yayyage.
Kamata ya yi a ce da zarar ‘ya’yanki sun tashi da safe, sun yi sallah, sun karya kumallo, to, kama su ki masu wanka, idan kuma ba ke ki ke masu ba, to, ki tabbatar sun yi wanka sun sa kaya masu tsafta.
Idan kuma ɗanki na goye ne, to, da ya tashi ki sa ruwa ki masu wanka, ki kuma ɗauke shimfidar fitsarinsa ki wanke, kar ki ce za ki bar su sa wani lokaci domin yin hakan na iya sa ɗakinki ya riƙa zarni wanda shi ma warinsa na iya cutar da ke da iyalinki haka kuma za a riƙa gudun shiga ɗakinki.
Har ila yau, kada ki riƙa barin wanki ya taru da yawa ba tare da an wanke su ba.
Uwargida ki kula da makwancin maigida, ki tabbatar cewa, kullum ɗakin shi a share yake, kuma a riƙa canzawa tare da wanke shimfiɗu a kan kari. A kodayaushe mijinki ya dawo gida, to, ya kasance ya sami komi naki bisa tsari. Tsafta na ƙara damƙon soyayya, haka kuma rashinta kan sa mijinki ya riƙa nesa-nesa da ke da ma ‘ya’yanki har ma ta kai ga a kullum, yana Allah-Allah ne ya bar gidan, ba kuma zai so ya dawo da wuri ba balle kuma har ya shigo da abokansa.
Saboda haka uwargida sai a kiyaye. Tsafta cikon addini!
Source Duniyar komputer