Kotun 'yancin dan Adam ta Turai ta yi watsi da hujjar wata ma'aikaciya wacce ta ke so ta rika sanya hijabi a wajen aiki.
An kori Christine Ebrahimian, daga asibitin Paris ne saboda ta dage a kan cewar sai ta rika sanya dan kwali.
Asibitin dai ya ce ya samu korafe korafe daga wajen marasa lafiya a kanta.
Dokokin Faransa sun hana duk wani ma'aikaci sanya wata alama da zata nuna cewar shi mabiyin wani adini ne.
Kotun dai ta ce ba aikinta ba ne ta yanke hukunci a kan dokokin aiki kuma ta yi watsi da rokon a kan hukuncin da aka yanke tun fari.
Title :
Kotu Ta Hana Wata Ma'aikaciya Sanya Hijab A Faransa
Description : Kotun 'yancin dan Adam ta Turai ta yi watsi da hujjar wata ma'aikaciya wacce ta ke so ta rika sanya hijabi a wajen aiki. An kori Ch...
Rating :
5