Ta zuba masa ido tana hankalta da tarin damuwar dake kwance a saman fuskarsa. Adaidai lokacin yake amsa gaisuwar kannensa,sannanya k'arasa har inda mahaifiyarsa ke zaune,cikin ladabi irinta Jafar ya russuna a gabanta ya gaisheta. Hajja ta amsa har lokacin idanuwanta basu kaura daga kan fuskarsa ba. Gefenta ya zauna yana mai yamutsa fuska alamar gajiya.
Hajja ta umarci d'aya cikin kannensa data kawo mishi ruwa.
Saida Jafar yasha ruwan nan mai sanyi sannan ya iya sauke numfashi.
Hajja ta jefo masa tambaya
"Babana menene ya faru na ganka cikin damuwa?"
Jafar ya shafi sumar kansa yana murmushi a wahale
"Babu komai Hajja,Siyama ce bataji dad'i ba. Ina kasuwa anti rumaisa ke sanarmin,a asibiti ma na iskesu har Hajiya. Amma jikin yayi sauki sun maidata gida."
Hajja cikin nuna jimami tace
"Assha, ai fa naji yarannan sunce Rumaisa tazo sun fita da Hajiyar(dayake gidansu Jafar da nasu Siyama suna facing juna) ashe wajenta suka nufa,meya samu ita Siyamar?"
Jafar ya d'an tab'e baki
"Wai juna biyu take dauke dashi."
Cike da mamaki hajja take dubansa
"Wai fa kace?"
Yayi saurin gyara zancen
"A'a,juna biyun ne Hajja."
Ta saki fuska "Alhamdulillah,nayi murna. Allah Ya rabasu lafiya,saika kula da ita sosai don Allah."
Jafar ya gyada kansa,Hajja dai ta lura ba rashin lafiyar Siyama kad'ai bane damuwar Jafar,don haka tace
"Babana akwai abunda ke damunka bayan wannan,ka sanarmin menene ke faruwa? Idan bani da maganin abun sai na bika da addu'a."
Tayi shiru cikin yanayin damuwa,ba yau ne farkon fara ganinshi cikin yanayi haka ba saidai batason sanya ido duk da tana zargin zamantakewarsu da Siyama sanin halin da akayi auren Hajiyarta bataso.
"Hajja bakomai,kaina yake ciwo ne. Ina kasuwa rashin lafiyar Siyama ya taso ni,amma yanzu komai da sauki. Idan da abinci a zubomin."
Ya k'arasa yana kwantar da kansa jikin kujera,idanuwansa a lumshe,bayason ganin hajjarsa cikin damuwa ko yaya ne balle kuma ace sanadinsa ne ta shigeshi. Yana ji sadda tace"Allah Ya yaye maka." A zuciyarsa ya amsa,ta kwalawa kanwarsa kira sannan ta bata umarnin kawo mishi abinci. Jafar kuwa ya rasa takaiman abunda zai kokawa, bakaken maganganun da Hajiya ta gasa mishi ko kuwa da KAZAMAR GIDAnsa? Dakyar ya iya k'ok'arin had'iye damuwarsa saboda ganin Hajja tana neman sanyawa kanta tunani duk a dominsa.
Bai bar gidan ba sai bayan isha'i bayan ya shiga sun gaisa da Alhajinsa yake sanar dashi dalilin barinsa shago da wuri. Alhaji yace sam,basuyi waya da ibrahim ba ballantana ya sanar mishi. Shima yayi farin ciki da cikin Siyama a karshe sukayi sallama ya tafi ko kallon gidansu Siyama baiyi ba tunda yasan Abbanta baya garin don haka babu sauran wanda zai shiga dominsa.
**************
Koda ya dawo ya sameta tana baccin a d'akinta. Ya rufeta saboda sanyi sannan ya wuce d'akinsa. A daren bacci b'arawo ne kawai ya saceshi.
******
Tun Jafar yana daurewa Siyama har yazo ya share zancen suka d'inke kamar basu ba.
Matsala ta farko daya soma cin karo da ita tun samun cikin Siyama,bai wuce k'azantar jikinta daya k'aru ba. Dole ya kauracewa hada shimfid'a da ita,idan kuma yaga cutar zatayi mishi yawa yakan rok'eta akan ta taimaka tayi wanka,harma da kanshi ya d'ora mata ruwa,sai ta gama kumbure kumburenta zatayi,kamar da gaske za'a d'ore a hakan sai kuma ta bar yi. Koda ya dora ruwan hakanan saidai ya hakura. Akan dole ya sabarwa kansa da azumin litinin da alhamis. Sunfi sati uku rabon da wata mu'amalar kwanciya ta shiga tsakaninsu,hakanan kowannensu yana nasa d'akin.
Siyama ta bar yin kowane gyara ga jikinta,idan kuwa unguwa ta kamata saidai ta goge hammatarta da ruwan alimun da lemun tsami,alokacin ne zata kokarta ta sharce gashinta wanda Jafar bai tab'a ganinsa a kitse ba. Duk wani kwaskwarima Siyama tasan yanda zata yishi muddin ta tashi fita unguwa.
Yanzun ma fitar ce ta taso mata,wai zataje gidansu daganan su wuce biki can a dangin hajiyar tasu. Yana tsaye gaban madubin d'akinsa yana aikin gyara sumarsa,ta shigo d'akin. K'amshin da yaji ya bugi hancinsa ne ya sanyashi waigowa. Murmushin takaici yayi ya k'are mata kallo tun daga k'asa har sama. Anci riga da siket,fuskar nan an wanketa da kwalliya daidai da zamani. Bai tab'a sanin ta mallaki kyakkyawan leshin nan ba sai a yau. Ya ganta tamkar Siyamarsa sak ta baya, abun bakin ciki harda wadannan kwalliye kwalliyan aka yaudareshi baisan kyallin banza bane.
Murmushi ta jefeshi dashi,ya girgiza kansa yana tab'e baki kafin ya juya ya cigaba da shirinsa. Hannuwanta yaji ta bayanshi
"Jafar banji kace nayi kyau ba?"
Ya lumshe ido ya bude,ta madubi suka kalli juna. Murmushi ya k'ara yi a karo na biyu
"Kinyi kyau,da ace haka kike zama a gidanki da ba haka ba. Kwalliyarki ai ta fita unguwa ce."
Ta sakeshi ta jingina da bango yayinda take dubanshi yana zura riga
"Jafar kenan,nikam kana bani mamaki yanda bakason yimin uzuri. Baka ganin yanda nake fama da kaina? Kwalliyar ma dole ce ta sanyani yinta a yanzun,kowane sutura zan saka inajin kaina a takure wallahi."
"Siyama kenan,kafin ki samu cikin kuma menene yake hanani yimin? Ko an fadamaki mazan waje sun fini bukatar kwalliyarki? Burinki ki k'ure adaka ki fita amma bakisan kiyimin a gida ba ko?"
Ya tabe baki yana daga kafada
"Ai shikenan,zan auro wacce zata dunga bani kulawa."
Ai saita daure fuska
"Zaka fara ko? Daman ku maza duk abunda matanku zasuyi maku bakwa tab'a gani. Duk kokarin da nakeyi baka gani Jafar. Ni banyi korafin yanda bakason cin abincina ba matukar ba shinkafa da wake nayi ba,sai kai keda bakin cewa banason yi maka kwalliya? Sau nawa ka bani kud'in kayan kwalliyar?"
Jafar dake shirin sanya hula ya tsaya cak yana kallonta,mamakima ta bashi. Ta dauke idonta daga gareshi fuskarta a kumbure
"Siyama har kina da bakin gayamin haka? Ai kuwa idan har kika shaideni akan bana siya maki kayan kwalliya duk da har yanzu akwai sauran na lefenki bakiyi adalci gareni ba. Hakanan sau nawa na baki kud'in wanke gashi kike biyan bashi dasu? Sau nawa kikayimin karyar zakiyi kunshi na ciro kud'i na baki,kin tab'a yi? Bani mantawa bikin Kawarki daya tashi kad'ai ne sadda na soma ganinki da kunshi a kafarki tun bayan na bikinki daya goge. Siyama ke ta dabance ma acikin kazaman matan,bansan irinki ba! Girkin da kike magana a zatonki zan iya cin cima marar dad'in d'and'ano ne? Ke komai da mata sukeyi ke bakiyinsa,baki iya ba sai afkin karance karance da kallace kallace. Duk a banza Siyama,banga amfanin ilimin boko dana arabin da kikayi ba. Bazan iya cigaba da zama kodayaushe ina yawon zuwa gidan abinci ba,ya rage naki ki gyara kanki ko kuma abunda kike gudu ya faru."
Har ya kai k'arshe bata da niyyar cewa komai. Binsa kawai takeyi da kallo,fargabanta ya k'aru. Kada dai ace dagaske Jafar auren zaiyi? Tana ganin ya fita waje, tayi saurin daukar wayarsa. Duk iya lalubenta bata ci karo da lambar wata budurwa ba 'bare' wacce bata sani ba yan uwansu ne zallah wadanda itama ta sansu. Tana shirin duba b'angaren sak'onni ya shigo. Yana kallonta saima ta bashi dariya yayi murmushi
"Fito muje,ba saikin wahalar da kanki ba Siyama. Bani da budurwa bana sha'awar yin wani auren amma ina sha'awar mace mai tsafta wacce ta iya girki da kwalliya. Wacce zata bani kulawa da girmana a matsayin mijin aurenta. Matukar zaki zama irin haka toh wallahi fargaba ba naki bane,domin babu macen da zata burgeni. Ke kanki kinsan bana ra ayin mata biyu. Amma kuma a yanzu na soma chanja ra ayi matukar bazaki gyara ba."
Ya d'auki wayarsa data ajiye,ko kallonta baiyi ba ya fito.
"Kin tsaya,nace ki fito zan rufe d'akin ko?"
Ta fito a sanyaye tana duban fuskarsa dake a had'e,ya rufe d'akin gam da mukulli tayi azamar riko hannuwansa. Bayason duban kwayar idanunta yanzun nan sai fushinsa ya sauka. Ta narkar da murya
"Jafar nasan bana kyautata maka,kayi hakuri don Allah. Ni yanzu ya kakeso nayi? Duk ka sanyayamin jikina Jafar,kaima kasan ban taba son wani mahaluki ba saikai,irin son da ko kusa bana marmarin wata ta kusanci inda..."
Ya katseta yana dariya,wallahi Siyama fa ta rainashi. Yo banda raini har ma ta tsaya tana tsarashi akan abunda yasan ba gaskiya bane. Shi yasan ba kud'i ne dashi ba sai rufin asirin Allah,ba wani kyau ne dashi ba na azo a gani domin a kyawun ma Siyama ta tsereshi ba kusa ba. Zai iya yarda tana sonshi saidai bayan aurensu ta rage sonshi tunda har bazata iya faranta mishi ba hakanan sonta ya ragu a zuciyarsa saboda sabbin halayenta da yaci karo dasu bayan auren.
"Kina b'atawa kanki lokaci,kin sameni ina bacci kin matsamin nayi sauri nayi wanka ana jiranki,yanzu kuma zaki tsaidani ina fa da wurin zuwa Siyama. Taho mu wuce,idan muka dawo sai ayi maimaicin karatun ko Allah zai sa yau nayi dace."
Ya janye hannuwansa yayi gaba,ta bishi a baya gwuiwa sake.... !
Zaune suke akan benci gaban gidan amininsa,Haris.Kwanansa d'aya da dawowa daga Gusau garin iyayensa. Hira sukeyi na bayan rabuwa,Haris yace
"Ina amarya Siyama? Ka k'i kawota su gaisa da Ummina ko?"
Ya harareshi
"Ita Ummin meya hanata kawo mana ziyara?"
Haris yayi dariya
"Zaka take gaskiya kenan? Ummina fa zuwanta biyu gidan a rufe ba kowa kodai ka manta ne? Idan zumuncin na gaske ne kaine yafi dacewa ka dauko Siyama itama tasan hanyar gidana."
Jafar ya mutsistsika hancinsa
"Wannan kuma sai damar hakan ta samu. Ni yanzu ka saurareni inada muhimmin batun da nake neman shawararka akai."
Haris ya nutsu yana gyara zaman 'medical glass' d'insa
"Ina sauraronka."
Jafar ya numfasa ya labarto mishi kad'an daga cikin matsalar da yake fuskanta a wajen Siyama. Ya k'ara da cewa
"Nifa na soma gajiya Haris,a ganina lokaci yayi da zan sanarwa iyayenmu. Watakila idan anci sa'a ta ji maganarsu."
Haris kallonsa kawai yakeyi,tun soma jin irin matsalolin da amininsa ke fuskanta, ya gyara zaman gilashinsa yafi sau biyar. Ba don shi da kansa ke sanar mishi ba babu abunda zai hanashi k'aryatawa. Bayan kammala sauraron Jafar yafi mintuna biyu kafin ya motsa bakinsa.
"Jafar kana nufin dukkan abubuwan daka lissafo halayan Siyama ne babu abunda ka k'ara akai?"
Jafar yayi murmushi
"Da ace kasan Jafar a makaryaci Haris,shine zakayi wannan tunanin. Kai shaida ne akan son da nake yiwa Siyama,ta yaya zanyi mata k'age? Haris shawara zaka bani,menene ya kamata nayi na kawo k'arshen matsalar nan?"
Haris ya numfasa
"Kaicon Siyama,na tausayawa rayuwarka Jafar. Babbar matsala ce wannan wanda ba kowane namiji ne zai iya juriyarsa ba. Hakika cigaba da rayuwa a haka ba shine mafita ba,baka da laifi ko a wurin Allah tunda har kayi mata nasiha ka kuma bita da fad'a amma duk da hakan tak'i chanjawa. Shawarar da zan baka itace,ka kai maganar zuwa ga yayarmu anti Habiba(firstborn a d'akinsu Jafar). Ka fayyace mata komai na tabbata bazata rasa taimakon da zatayi gareka ba amma kada kace zaka sanarwa iyayenku,ka manta da yanda akayi auren ne ba'a son ran Hajiya da wasu ba? Ko kuwa so kake ayi maku dariya?"
Jafar ya jinjina kai,hakika shawara ma tana da dad'i. Ba da ban Haris ba,da tuni ya aikata ba daidai ba.
"Hum,damuwa ta sanyani gaza yin tunani mai kyau. Inda ace baka tunasar dani ba,nasan bazan bi takan anti habiba ba. Nagode da wannan shawarar,in sha Allah gobe zanje har gida na sameta."
Haris ya amsa
"Yauwa kokaifa,kasan fa halin wasu matan,yanzu kana kai k'ararsu maimakon su shiga taitayinsu sai wani sabon salon ya b'ullo. Gwara abi abun sannu sannu ko Allah zaisa a dace. Wallahi abun bai bar bani mamaki ba."
Jafar ya girgiza kansa
"Don baka gani bane,ni nasan yanda nake fama. Wai kuma a hakan ne ake cewa ana kishina."
Haris yayi dariya
"Kaicon Siyama,Allah Ya gyara."
"Ameen.
Title :
Kazamar Gida Part 4
Description : Ta zuba masa ido tana hankalta da tarin damuwar dake kwance a saman fuskarsa. Adaidai lokacin yake amsa gaisuwar kannensa,sannanya k'a...
Rating :
5