Kujera taja ta zauna tana fuskantarshi saidai kuma idanunta yana ga kwanukan abincin daya cinyeshi tas tana kallo cike da mamakin yanda mutum magidanci kuma sabon aure irin Jafar ace har zuwa yanzu bai bar ziyartar shagunan abinci ba. Ya katse mata tunaninta
"'Yar nijar abincinku yana k'ara dad'i koyaushe. Ai na dauka Mama ce karfin girkin sai yanzu na fahimci kema gwanar iyawa ce bayan kauracewar mama daga shagon."
Tayi dariya ta jinjina kanta
"Kaji fa yayana hum,nasan duk iya girkina ai bana kai antina ba ko?"
Yaji kamar da gayya tayi mishi tambayar. Kawai ya basar kamar baiji ba. Hannu yasa a aljihu ya ciro kud'i ya mik'a mata.
"Gashinan a ajiyemin d'an waken nan da rana zan lek'o."
Ganin zai mike tayi saurin magana
"Ni kuwa yayana inason tambayarka."
Jafar ya koma ya zauna yana mai fargabar tambayar da Ladi zatayi mishi duk da dai yasan ita d'in yarinya ce wacce tasan ya kamata saidai bayason tayi mishi tambayar abunda ya shafi iyalinsa. Ai fa ta dauko hanyar hakan.
"Yayana na fahimci kana tattare da damuwa. A kwanakin nan walwalarka ta ragu sosai,hirar nan ma da kake d'an yi ka bar yinsa."
Jafar ya tsayar da dubansa ga Ladi,akwai ta da saurin fahimta. Ya daure ya k'ak'alo murmushi
"Ke kam 'yar nijar ba dai fahimta ba. Kwana biyun ne banjin dadin jikina wannan shine babban dalilin chanjawata."
Ladi ta rausaya kanta ko kad'an bata yarda da zancen Jafar ba.
"Ina mai baka shawara akan ka dunga kokarin danne damuwarka ko don saboda mutane. Yanzun nan sai su soma zargin wani abu daban wanda bai zamto damuwarsu ba ,hakanan zasu sanya maka idanu. Addu'a takobi ce ga muminai,matukarzaka juri yinta toh ina mai tabbatar maka komai na rayuwarka zai tafi daidai. Allah Ya magance mana matsalolinmu gaba daya."
Daga haka ta mike ta had'a kwanukan bayan ta jefa kud'in a aljihun Apron d'inta.
Anan zaune ta barshi yana binta da kallon mamaki,zantukanta sun nuna lallai bata yarda da hujjar daya bata ba. Ya zaiyi toh? Koda ace k'arya bata daga cikin halayensa hakanan dai yake koyon yinta ba don yaso ba. Ai abun kunya ne ma ace ya soma fadin matsalar gidansa tun bai shekara da matarsa ba. Maganar Ladi ta shigeshi sosai ya k'udura a ransa dole ya rage zuwa shagon saboda lallai batayi k'aryar ba, mutane sun soma gulmarsa har akwai wani cikin abokan kasuwancinsu ya taba jifansa da magana akan yayi aure bai bar kwasar k'afa yawon bin abincin siyarwa ba.
Dakyar ya mik'e ya koma bakin aikinsa. Da ranar ma bai iya dawowa yaci ba saboda nauyin da yakeji akan maganganun Ladi.
Auren mace irin Siyama bashi da riba. Me za'ayi da KAZAMAR GIDA?
********************
Jafar bai shigo gidansa ba sai k'arfe takwas na dare. Zuciyarsa shige da fargaban kalar kazantar da zai tarar. Ya faka mashin d'insa ya rufeshi sannan ya shiga ciki.
Inji ne yake ta aiki,ya duba yaga an kawo wuta ya chanja hanyar. Ya kashe injin,da gudunta ta fito daga d'akin
"Wa...?" Ta fasa k'arasawa ganin Jafar ne. Tsaki taja ta koma d'akinta. Jafar takaici ya isheshi,yakai dubansa ga tsakar gidan,babu laifi tayi shara saidai ba'a wanke dustbin d'in ba. Kaca kaca yake jikinsa,yakai dubansa ga kayan wanke wanken. Bata dauke ko cokali ba,saima wasu kayan da aka k'ara lodasu a bakin makwararar ruwa. An wankesu an barsu anan. Cikin fusata ya bita cikin d'akin. Babu laifi falon domin k'arnin ya tafi sai abunda ba'a rasa ba. Ga kayanta nan wankakku kwanansu biyar kenan da kawosu daga wajen mai wanki amma Siyama bata da niyyar maidasu mazauninsu.
Kansa yaji yana sarawa,ya dubeta. Shimi ce a jikinta wacce daga kalar fara ta koma ruwan k'asa tsabar datti,sai wani shegen dogon wando marar kyawun fasali data sanya,kwakwa take b'antala da hak'orinta. Tana ci hankalinta yana ga kallon wani film na turawa.
Yasa hannu ya kashe socket din gaba daya ta jikin bango kafin ya k'ara maido dubansa gareta. Kafin yayi magana ta rigashi
"Haba Jafar,wai menayi maka ne? Wace irin tsana kayimin da kake kokarin hanani sakewa a gidan nan? Tun safe kake nemana da fitina ina kyaleka! Wannan wace irin rayuwa ce! Matukar zaka cigaba da musgunawa rayuwata bazan fasa gasa maka magana ba!"
Siyama ke maganar a matukar fusace,da alama dai tun safe tana kullace dashi. Tana kaiwa aya ta nufi hanyar d'akinta tun batayi taku uku ba taji ya damkota ya yo baya da ita. Nan ta zube akan kujera. Ta dubeshi cike da masifa,da sauri ya tareta cikin kaushin murya
"Idan kika k'ara cewa uffan siyama! Saina yi maki dukan kawo wuk'a naga wanda zai kwaceki!"
Ta maida bakinta tayi shiru tana huci,tuni ta soma kuka ita kam batasan Jafar mugun mutum bane sai bayan aurensu. A baya tana daukarsa mutum mai sanyi ashe dai munafuntarta yayi sai yanzu take gane ainahinsa.
Cikin d'aga murya Jafar ya soma magana
"Siyama baki da hankali! Nace baki da hankali! Babu ranar da zaki dawo hayyacinki sai nakai ga fallasa irin rayuwar kuncin da nakeyi dake a wajensu Abba! Nasan shi kad'ai ne zaiyimin maganinki! Dubi kayan can Siyama(yayi mata nuni da yatsa),kwanansunawa ajiye anan?! Kiyi duba da suturar dake jikinki! Haba siyama! Kin shayar dani mamaki kwarai dagaske!
(Yaja hannunta da karfi zuwa tsakar gidan)
"Wa kike jira yazo ya adana maki kayan can a kicin?? Wane bawa kika ajiye? Meyasa kika bambanta da sauran mata ne? Ana batun kazaman mata ban tab'a cin karo da KAZAMA irinki ba Siyama! Kyawunki ya tashi a banza! Ina yi maki kallon wacce tafi kowa iya k'ure adaka a baya ashe kyalkyalin banza ce ke! Ni Jafar ba kazami bane inason tsafta da mai yinta! Ina gaggauta baki shawarar ki gyara idan kuwa bazaki gyara ba lallai ki sani zan fayyacewa Abba irin zaman da mukeyi dake!"
Yana gama fad'in haka ya bud'e d'akinsa ya shige. Gaba daya ransa yana k'una,ya rage kayansa ya fito da niyyar shiga wanka. Tana nan har lokacin a durkushe tana kuka,ko kallonta baiyiba.
Gaba daya abun ya isheshi,kodayaushe ace mutum da gidansa amma yana fargabar shigowa saboda bai san kalar kazantar da zai riska ba? Ya ja tsaki alokacin da ya fiddo k'ullin namansa a ledar da tun shigowarsa take a hannunsa. Zama yayi yaci ya koshi yasha ruwa. Sai a sannan ne nutsuwa ta zo mishi,don har ga Allah a fusace ya shigo gidan. Yana son Siyama saidai fa ya soma gajiya da d'abi'unta,cikikuwa harda rashin daukarsa da k'ima a idonta.
Yana kwance yana tunane tunane yaji ta turo kofar ta shigo. A hankali ya lumshe idonsa,baya kaunar ganin fuskarta ko kusa.
Yana jin lokacin data zauna a gefen gadon baiyi ko niyyar bud'e idanunsa ba ballantana ya dubeta. Ta narkar da muryarta
"Jafar."
Bai amsa ba sai ma ya juya mata baya. Ta cigaba da magana
"Jafar kayi hakuri don Allah,nayi kuskure amma zan gyara kaji? Don Allah kada ka sanarwa Abba."
Sai lokacin ya bude idanunsa,ba tare da ya juyo ba yace
"Sau nawa kike fad'in zaki gyara Siyama? Sau nawa zanyi ta bibiyarki,wane irin nasiha ne ban yi maki ba? Inace har kasussukan wa azizzika na sayo maki na kawo? Wane taimako ne banyi maki ba Siyama? Haka kikaga hajiyarki tana yi? Ban taba zuwa gidan hajiyarki na sami gidanku da kazanta ba,ke kanki ban taba ganinki a hargitse ba. Menene dalilin chanjawarki? Meyasa bakyason gyaran gidanki? Siyama ya kikeso nayi? Abinci kansa ace na waje yafi wanda za a girka a gidana dad'in d'and'ano? Wace halaka kikeson jefa kanki da ni?"
Ya mike zaune ya juyo ya dubeta,ta chanja suturarta zuwa doguwar rigar bacci. Hannunta ya riko yana kallonta idanuwansa da suke a rine da bacin rai,kamar mai shirin kuka yace
"Dubeni Siyama! Ki dubi mijinki! Ke yanzu ko a ido bai chanja maki ba? Ina kikeso na samu nutsuwa da farin ciki bayan a wajenki? Soyayyar da muke yiwa juna da alk'awarurrukanda mukayi gabannin aurenmu cewar zamu kyautatawa juna ina suka tafi? Na gaji da zama da wannan siyamar,nafisonSiyamata ta ainahi ta dawo. Domin Allah Siyama ki chanja hali,ki gyara ki zamto mace mai tsafta da kula da miji,ki fita layin kazaman mata. Kinmin alk'awarin zaki chanja?"
Siyama wacce tayi lakwas tana sauraron Jafar har yakai aya,tana kaunar mijinta sosai hakanan tana tsananin kishinsa(kuji fa),ta share hawayenta
"Zan gyara Jafar,kaima don Allah ka rage fad'a banaso yakan tunzura zuciyata."
Jafar yayi murmushi
"Ke kike sanyawa nayi maki Siyama. Amma ba don naso ba nake aikatawa. Komai ya wuce."
Siyama ta saki murmushin dake k'ara fiddo da kyawun halittar ta
"Nagode Jafar,na kawo maka abincin ne? Favourite dinka nayi,tuwo ne."
Da sauri ya dakatar da ita,bai mance d'and'anon miya nata ba
"No,bar abincin nan. Da safe saiki d'umama min ko?"
Tayi murmushi.
****************
Da safe kamar kullum,Jafar ne ya soma tashi. Yakai dubansa ga Siyama,tana kwance tana sharar bacci tun bayan sallar asuba da sukayi jam'i. Murmushi yayi ya girgiza kansa,ai mai hali dai baya fasa halinsa. Ficewa yayi ya shiga kicin ya d'ora ruwan wanka. Sannan ya tsaya a tsakar gidan kamar mai tunani,sai kuma ya koma d'aki ya cire jallabiyarsa ya fito daga shi sai gajeran wando ya soma aikin gidan. Dakunanta ya soma gyarowa,ya had'a tulin kayan wanki waje guda ya k'ullesu. Sannan ya fad'a bandaki. Da gudu ya dawo baya yana numfarfashi. Can dabara ta fado mishi,ya dauki d'ankwali ya d'aure hancinsa ya fad'a ciki. Hankalinsa ya tashi ganin ledojin pads a hanyar makwararar ruwan,da alama ciki take turasu duk lokacin data fidda. Yaja tsaki yafi a k'irga,gaba daya tsikar jikinsa ta tashi,ya fito daga bandakin a guje jin da yayi amai yana taso mishi kamar mai sabon ciki. Wurgi yayi da dankwalin gefe yana maida ajiyar zuciya. Innalillahi,ashe Siyama abun nata haka yayi yawa? Gaskiya babu ta yanda zai iya kimtsa bandakinta,dakyar ya dawo daidai sannan ya fada d'aya band'akin,shi kam da sauki kawai wanki yake buk'ata. Jafar ya zage ya durza ko'ina bayan yayi flushing. Saida ya tabbatar ya wanku ya shiga na ukun ya wankeshi tsaf.
Alokacin da ya sharo d'akuna ya dawo falo da niyyar sharewa,yana yi yana tari saboda k'ura, Siyama ta shigo tana murza idanu,ta dubeshi
"Ah,jafar ai da ka bari tunda nace zanyi ai zanyi ko?"
Jafar cike da takaici yace
"Fita Siyama,idan na kammala kizo akwai aikin da zakiyi. Dubamin ruwana tukunna."
Ta juya ta fita zuciyarta cike da murna don daman ta kwana tunanin ta inda zata soma wannan jan aikin.
Bayan jafar ya had'e sharar har dana tsakar gidan,ya zuba a shara sannan ya wanke hannunsa. Siyama ta kashe ruwan ta barshi anan. Tana kallonsa ya shiga d'akin ya fiddo turarukan tsinke ya kunnasu ya sanya a duka d'akunan da falo. Nan da nan k'amshi ya mamaye gidan. Sai lokacin ya sharce gumi ya dubeta
"Zo kiga aikinki."
Suka shiga har d'akinta,ko'inayayi kyau sai k'amshi da iska mai dad'i,Jafar bai karasa ciki ba yace
"Shiga bandakin nan Siyama,ki cire abunda kika cuccusa wajen wucewar ruwa,ki gyara komai ki wanke. Hakanan kicin yana bukatar gyaranki. Tsakar gidan nan ma ki wankeshi please,banason ganin wannan dank'o dank'on kinji ko? Sannan kafet din falon nan dana ciro,zan sanya azo a dauka akai wanki."
Ta gyada kanta,ranta babu dadi. Babban abunda ke tayar mata hankali kenan. Itama kanta kyankyamin band'akin nata takeyi. Murnarta ta ragu domin tayi zaton ma ya gyara,kicin kuwa ko almajirinta ne zata sanyashi ya gyara ya wanke tsakar gidan. Koda a kudin cefane ne ai saita biyashi.
Jafar yayi wankansa ya shirya kamar koyaushe,bayan ya tabbatar da tsabtar bandakinsa ya fito ya kulle abinsa,cike da nishad'in ganin tsakar gidan tsaf ya fada dakinsa. Nan kuwa bai tsaya yin shara ba a zummar sai ya dawo daga kasuwa......
Hmm kap allah raba..!