Gabansa ya fad'i da jin tambayar da Hadiyya ta watso mishi. Ya daure ya k'ak'alo 'yar dariya
"Kedai akwai ki da wasa,haba ni dan adam me zanyi da aljana ina da kamar Siyama?"
Ya fad'a cikin son maida zancen wasa. Tayi dariyar itama wanda ya taho da ruwan hawaye ta jinjina kanta zuciyarta na tururi,ta daure tace
"Sau nawa kuma akayi hakan? Kaga sai a k'ara dank'on zumunci "
Yayi dariya
"Lallai kam."
Daga haka ya bagarar da zancen kamar bai fahimci iyakar gaskiyarta take fad'a ba. Tun ba yau ba ya fahimci son da takeyi mishi hakanan bayaso ko kadan ya gaskata yanayin da yakeji game da ita.
Itama Hadiyya ganin ya share maganar ne ya sanyata yin dana sani. Tasan shikenan Jafar bazai tab'a sonta ba,daman zuciyarta ke yaudararta har ma take ganin kamar so ne yasa mu'amalarsu tayi k'arfin da har ya nemi sanin gidansu. Ashe ashe ba haka bane. Ji tayi gaba d'aya hirar ta gundureta,don haka ta katseshi da fad'in
"Bacci ya taho yaya j,zan kwanta saida safe."
Jafar shi kansa yana bukatar tunani,don haka ba musu sukayi sallama ya jona wayar a chaji. A sannu ya maida kai ya kwanta zuciyarsa cike da tunani. Hadiyya sonshi takeyi? Meyasa baiji haushinta game da hakan ba kamar yanda yakejin haushin sauran yan matan irinta masu nuna suna kaunarsa? Toh kodai shima yana sonta ne?
Ya girgiza kanshi da sauri ya k'ara muskutawa
"Bazai tab'a yiwuwa ba. Bayan Siyama babu wata d'iya mace da zan nunawa so. Babu!"
Ya fad'a a fili,cikin son kawar da tunane tunanensa,yayi addu'oinsa ya rufe ido har bacci ya daukeshi.
**********
Batayi mamakin ganin Mamanta tsaye a kanta ba saboda kukan da takeyi mai k'arfi ne. A firgice Mama ta k'araso falon ta zauna tana dubanta.
"Ladi kina cikin hayyacinki kuwa? Meke faruwa ne?"
"Bakomai mama,um...um...nayi mummunan mafarki ne."
Mama tace
"Haba Ladi shine saiki dunga kuka haka kamar ba musulma ba? Addu'a ya kamata kiyi,sannan ko menene kika gani ai iyakarsa mafarki ba wai gaske ba. Allah Yayi mana tsari da sharrukan dake cikin mafarkanmu,Ya tabbatar mana da alhairansa."
Dakyar ta iya amsawa,mama tace
"Tashi muje ki kwanta,kafin nan ki d'ora alwala"
Tabi bayan mamanta bayan ta kashe wayar ta ajiye anan kan kujera. Bata marmarin sake bud'e wannan wayar,bata da amfani tunda wanda takeso baya sonta. Ta tabbata cigaba da sauraron Jafar k'arin tashin hankali ne ga rayuwarta. Ka hak'ura da duk wanda zai nuna baya sonka,shine mafita...!
********
Kwana uku da yin haka tsakanin Jafar da Hadiyya. Ya shiga damuwa kwarai na rashin samunta a waya. Har mamakin lamarin yakeyi,toh menene kuma na damuwa har haka? Daman ai koda bata barshi yanzu ba wataran dole fa zatayi aure su rabu. Saidai wannan baisa ya bar damuwar rashin samun wayar Hadiyya ba. Gashi ko gidansu bai tab'a zuwa ba,kamar yanda ko a hoto basu san junansu ba ballantana ya sanya ran wataran zai iya had'uwa da ita.
Ita kuwa Ladi kacokam ta maida hankalinta ga karatunta duk da cewa can k'asan zuciyarta tunanin Jafar ne mamaye. Kwana ukun nan ko shago bata bin Mama suje tana fakewa da gajiyar makaranta. Babban dalilinta na gujewa shagon bai wuce fargabar yin tozali da Jafar ba,batason ganinsa ya fama mata wani mikin. Daman yanzun ma wane irin wahala ce bata sha? A kwana ukun nan gaba d'ayanta ta rame,tsananin kewar muryarsa takeyi. Saita dauko wayarta a yini fin sau goma da niyyar bud'ewa amma data tuna cewar son maso wani takeyi wanda takeso bai damu da ita ba kawai sai ta fasa. Ta koyawa kanta yawan duba darussan makarantarsu,babban takaicinta ga Basma tayi mata nisa balle ta nemi shawararta. Ita kad'ai take kid'a da rawarta. Mahaliccinta kad'ai Yasan matsalarta.
******
Ranar wata litinin ta yanke shawarar zuwa kasuwa ko don kautarwa da Mama damuwar da ta sanyawa zuciyarta akan rashin sanin dalilin chanjawarta.
Ganinta kuwa ba k'aramin farin ciki yasa Mama ba. Ladi tayi iyakar kokari wajen danne damuwarta saboda Mama. Cikin ikon Allah ma sai ya zamana a ranar ko k'eyarsa bata gani ba.
*****
Bama shagonsu Ladi ba,ko kasuwar Jafar bai lek'o shigeta da wuri ba sakamakon kiran daya samu daga Hanif,inda ya sanar dashi Siyama ta haihu da asuba anan asibiti. Farin ciki marar misaltuwa ya mamaye Jafar,cikin fad'a yace "Amma meyasa tunda aka mik'ata asibitin babu wanda ya sanarmin?"
Hanif yayi dariya
"Toh inda an sanar maka me zakayi? Ai fad'ar haihuwa yafi dad'i akan nakuda. Ka garzayo dai kaga d'anka mai kama dakai."
Jafar yayi tsalle ya sauko daga gadon. Tuni ya mance da damuwar da yake ciki na rashin jin Hadiyya.
Acan kuwa,daga Hajiya sai Amina matar Hanif ya tarar. Lokacin karfe bakwai da rabi na safe.
Jafar yayi murnar ganin Siyama da d'ansa cikin koshin lafiya. Anan waje ya zauna yayi ta kiran 'yan uwa da abokan arziki bai damu da yanda Hajiya ke kananun maganganu ba. Wai ko nauyinta baiji ba ya sungumi jaririnsa har yana sumbata.
Kafin kace me,tuni yan uwa sun cika asibitin. Hajja kanta saida tazo.
Jafar bai bar asibitin nan ba sai wajen uku na rana,saida yaci abinci yayi nak sannan ya tafi kasuwar cike da farin ciki. Ko ta kan shagonsu Mama bai bi ba,hankalinshi duka yana ga mai jego da d'ansa.
Da yamma aka sallamesu suka koma gida. Wannan yasa Jafar yana barin kasuwa bai zarce ko'ina ba sai gidansu...!!
Yakai mintuna talatin suna hira da Hanif a babban falon Hajiya,saidai babu niyyar za'ayi mishi magana da mai jego ko kuma a mik'o mishi d'ansa. Hanif yaje har wajen sau uku saidai amsar an musu wanka,tana cin abinci,ana gyarawa baby jiki. Can dai yaga abun bana k'are bane dole ya mik'e,hanif ya dubeshi
"Ba dai tafiya ba?"
Jafar yayi murmushi
"Eh zan shiga gida daganan zan wuce."
Da sauri Hanif ya mik'e
"A haba ko baby baka gani ba? Jira don Allah bari nayi musu magana."
Jafar ya koma ya zauna,yana jiyo shewar Rumaisa dasu Amina matar hanif. Hira sukeyi hankali kwance.
Hanif ya shiga ya samesu,ganin Siyama zaune kawai,yaron yana cikin gadonshi ransa ya b'aci.
"Ke wane irin iskanci ne tun d'azu mijinki yana zaman jiranki amma kin gaza fitowa? Idan ma baki da niyyar zuwa ai saiki bashi yaronsa ya gani ko?"
Siyama ta mike don daman Hajiya ce ta hanata fita tun d'azun sai fad'a takeyi ita bazata dauki rashin kunyar jafar ba,akan wane dalili zai dunga yin zarya daga haihuwa?
Ganin Hajiya batanan yasa ta fito,Hanif tuni yayi gaba da jaririn a hannu. Jafar ya karb'eshi yana dubansa,babu abunda ya bambantashi da yaron sai haske kawai da zai nuna masa. Sanyin dad'i ya mamayeshi yana jin kaunar yaron matukar gaske tana k'ara shigarsa.
"Ina wuni."
Ya d'ago ya dubeta fuskarsa dauke da murmushi
"Lafiya lau mai jego,ya jikin?"
Ta d'an yatsine fuska
"Jiki da sauki."
Ya lura tana cikin fushi,sai ya tambayeta
"Yaya dai? Akwai wata damuwa ne?"
Ta girgiza kanta har lokacin bata saki fuskarta ba
"Don Allah my j kada ka rinka zuwa akai akai,Hajiya har ta soma fad'a. Wai duka duka yaushe aka rabu a asibiti har ka biyomu? Ka bari sai mu dunga gaisawa a waya,koda ta kama zakayimin magana mai muhimmanci sai muyita a waya amma.."
Kallon da yake jifanta dashi ne ya hanata k'arasawa
"Shine dalilinki na k'in fitowa ko?"
Ya jinjina kanshi,duk wani murna da ya taho da ita da d'okin ganinta da d'ansa nan da nan ta kau. Ya mike ya mik'a mata yaron,ya sanya hannu a aljihu ya fiddo kud'i ya ajiye mata.
"Shikenan,nagode. Amma ki sani koda ban nemi ganinki ba zan nemi ganin d'ana wannan kuma babu mai hanani. Ke kam naji duk sadda kika bukaci ganina sai ki sanarmin. Amma bazan yarda da sharad'in nan ba daga haihuwa yau yau a kafamin shi. Bamai yiwuwa bane."
Ya juya ya fice rai a b'ace. Siyama taja tsaki,shi dai Jafar batasan irinshi ba. Banda zuciya babu abunda ya ajiye. Magana bata kai ta kawo ba zaiyi fushi. Ta mike ta koma d'aki.
*******
Hajja ta jefo mishi tambaya bayan ta gama lura da yanayinsa
"Kai kuma meya faru?"
Ya girgiza kai ya ja numfashi,nan ya labarta mata yanda sukayi da Siyama. Cike da mamaki Hajja tace
"Ikon Allah,daga haihuwa yau yau d'innan har an soma kafa doka? Allah dai Ya kyauta. Saika kiyaye don a zauna lafiya. Kaga kuma haihuwar fari ce,mata zasuyita zuwa saika rage shiga gidan."
Baice komai ba,Hajja ta ja shi da wata hirar game da tsarin da yayi nakai kayan barka a al'adance,
"Nikam bansan yanda kukeyi ba Hajja. Abunda yafi zan bawa anti kudad'e idan yaso sai ta had'a a mika musu."
Hajja ta gyada kanta
"Hakan yayi,Allah Ya k'ara rufa asiri."
"Amin."
*****
Bazata iya kashe kanta ba,ta lura tayi nisan da batajin kira akan sonsa. Wannan yasa tana dawowa daga shagonsu ta bud'e wayarta. Tayi mamakin jin shigowar sakonni har uku. Na farko daga kamfanin mtn ne,na biyu dana uku an turosu ne jiya da yau. Na biyun gaisuwa ce da tambayar lafiyarta daga Jafar. Na ukun kuwa,sanar da ita haihuwar Siyama yayi. Taji dad'in k'aruwar daya samu,don haka ta ajiye wayar da zummar idan ta idar da sallar isha'i zata aika mishi sakon taya murna.
Tana idarwa,mama ta lissafa kud'in adashi ta bata akan takai mata gidan hindatu mai adashi. Taji dad'in wannan aiken tasan ta samu damar siyan kati. Ta rarumi wayarta da hijabi ta fito. Saida ta soma biyawa ta sayi kati ta sanya,ta nemi gefe ta tsaya. Sak'o ta rubuta mishi ta aika sannan ta cigaba da tafiya kasancewar akwai 'yar tazara tsakaninsu da Hindatu mai adashi.
Babu dad'ewa wayarta ta soma vibrating ta duba,murmushi ya kwace mata zuciyarta na bugawa da sauri sauri. Yaushe rabonta da jin muryarsa? Da sauri ta d'aga tare da sallama.
"Deeya! Ina kika shiga ne kika manta da yaya j,bakya ko tunanin halin da zan shiga? Tabbas nayi fushi dake mai yawa."
Ta gimtse dariyarta,ta k'ara yin sallama a karo na biyu jin da tayi bai amsa na farko ba. Ya amsa mata,a hankali tace
"Yaya j,bari na isa gida zan maka flashing,yanzu ina kan hanya ne."
"OK."
Ta kashe wayar,tana mai jin wani irin farin ciki. Nan fa ta d'aga k'afarta har ta isa gidan Hajiya hindatu mai adashi. Injinsu sai aiki yakeyi,tana zaune a falon. Suka gaisa ta mik'a mata kud'in,Hajiya hindatu taji dadi,
"Shiyasa nakeson Binta,bata wasa. Takan bayar akan lokaci."
Dariya kawai Ladi tayi sannan ta tambayi Jamilah,diyarta. Ta nuna mata d'aki. Da saurinta ta nufi d'akin. Jamila tana band'aki,wannanya bata damar dannawa Jafar kira. Ko minti d'aya batayi ba ya biyo bayanta...
Uhmmm
Title :
Kazamar Gida Part 10
Description : Gabansa ya fad'i da jin tambayar da Hadiyya ta watso mishi. Ya daure ya k'ak'alo 'yar dariya "Kedai akwai ki da wasa,...
Rating :
5