Kwana biyu da yin haka,babu laifi Jafar yaga chanji domin yakan dawo ya tarar an share gidan. Hakanan dakunanta tun gyaran da yayi musu har lokacin bata b'ata ba amma sunyi k'ura saboda iskar ruwa da ake yawan yi. Bai ce mata komai ba ya bita a hakan. Ai da dai wannan shegen kazantar ya gwammace suyita tafiya hakanan da kansa ya dunga gyara inda baiyimishi ba.
*************
Tun ranar da Jafar yak'i waiwayar shagon take cikin damuwa. Ta rasa abunda yake yi mata dadi. Tana jin kanta a mai laifi,inama bata nemi sanin matsalar Jafar ba. Yanzu gashinan ya kauracewa shagon nasu duk da batasan dalilinsa ba saidai kwarai tana zargin kanta. Gashi har Mama ta dawo,rashin ganinsa baisa ta matsa da tambaya ba tunda a yanzu mijin aure ne. Saidai tana mamakin yanda bai zuwa su gaisa kamar yanda a baya yakan yi koda bazai ci abincinsu ba. Ladi ai ta fita shiga damuwa domin sau biyu tana zuwa nemansa a shago don mik'a mishi sauran chanjinsa amma bata samunshi.
Babu zato babu tsammani,ta shigo sanye da kayan makaranta wanda aka dinka hijibin har gwuiwa,ta hangoshi zaune a shagon yana cin abinci yana hira da Mama hankali kwance. Nan da nan ta sauke ajiyar zuciya,da saurinta ta k'araso ciki da sallama. Sai a sannan ne Jafar yasan da shigowarta,murmushi yayi mata
"'Yar nijar."
Tayi dariyar farin cikin ganinsa,Jafar yana burgeta sosai saboda mutuncinsa. K'arasawa tayi ta gaisheshi a ladabce ya amsa cikin sakin fuska. Ta juya ga sauran customers nasu ta gaishesu sannan ta maido dubanta ga Jafar
"Yayana nayi zaton fushi kakeyi dani,don Allah idan maganata ta rannan ta b'ata ranka kayi hakuri. Da ace nasan bazakaji dad'inta ba,bazan yi ba."
Jafar ya girgiza kansa
"Baki b'atamin rai ba Ladi,saidai wasu dalilaina ne suka sanya nabar lek'owa. Kiyi hakuri,ki bar zargin kanki. Ai ke Ladi baki da wata d'abi'a da zaki b'ata ran mutum dashi,kina da kaifin basira da hankali. Uwa uba gaki mai tsafta wanda.."
Ya sanyawa bakinsa linzami,idan baiyi takatsantsan ba yanzu sai yayi furucin da Ladi zata d'ago damuwarsa. Don haka ya share batun yana murmushi
"Ke dai kada ki damu kanki,bakiyi laifi ba kinji ko?"
Murmushinta ya fad'ad'u har ana hangen hak'oranta
"Nagode yayana,bari na barka ka kammala sannan kada kace zaka biya fa. Har yanzu chanjinka suna...." Ya katseta da hanzari
"Na bar maki 'yar nijar. Ki rik'esu ki siya powder."
Sukayi dariya,tayi gaba bayan tayi mishi godiya. Ranar kam zuciyarta fes.
*********
Da misalin hudu da rabi na yammacin ranar juma'a,Jafar yana tare da abokansa na kasuwa suna ta hira da shek'a dariya. Idan suka sami customers kuma sai hankalinsu ya koma garesu.
Ibrahim ne ya katseshi
"Kaifa tun dazu wayarka tana ringing."
Ya mike da sauri ya shiga shagon ya zaro wayar daga chaji zuciyarsa babu ko d'igon damuwa,saidai ganin lambar Rumaisa duk sai ransa ya b'aci. Duk a yayyun Siyama babu wacce jininsu bai hadu ba kamar ta. Itace kan gaba wajen yiwa matarsa hud'ubar rashin arziki,domin da kunnensa yasha jinsu a falo yayinda suke hira. Ba'ason ransa ba ya dauka,kafin yakai ga magana ta rigashi
"Haba Jafar,kasan sau nawa nake ta danna maka kira ne? Wannan bayi bane,saika dunga ajiye waya a kusa tunda dai kabar gidanka ba lafiya."
Nan take gabanshi ya fadi
"Kiyi hakuri anti,wayar na sanyata chaji ne. Meke faruwa a gidan nawa?"
Ai saita soma fad'a
"Lallai Jafar,wannan ya nuna baka kula da Siyama. Banda haka ace tun safe matarka take fama da jikinta baka da masaniya? Toh Allah Ya kyauta,idan kaga dama kazo ka samemu muna nan a asibitin Getwell har Hajiya."
Ai bai jira komai ba ya mike yana maida hularsa,ya dubi ibrahim
"Zan tafi asibiti ne madam babu lafiya,koda Alhaji yayi kiranka please ka sanar dashi."
Daga haka ya fice,abokansa suna tambayar lafiya saidai bai iya basu amsa ba.
Yana tuk'a mashin d'insa yana tunanin Siyama. Daman fa tun safe da ya nemi hakkinsa ta gudu daga d'akin zuwa nata,acewarta bacci takeji sosai. Hakan yasa ta k'ular dashi don hatta kud'in cefanan anan kan kujera ya ajiye mata. Yayi dana sanin biyewa mace,inama alokacin ya cusa kansa har d'akin domin bincikar lafiyarta. Duk da d'abi'un Siyama fa yana sonta sosai wannan ne babban dalilin hakurin da yake da ita.
Yana tunane tunanensa yana tuk'i har ya iso k'ofar asibitin ya faka.
Ko ciwon me siyama takeyi..?
Kai tsaye ya shiga asibitin,duk iya waige waigensa bai hangosu zaune ba. Wannan ya sanyashi fiddo wayarsa ya dannawa rumaisa kira. Bayan ta dauka ya nemi sanin inda suke. Lek'owa tayi,ya hangota ta fito daga hannun hagunsa. Fuskarta a daure,suna hada ido ta watsa mishi kallon banza sannan tayi gaba. Har zuciyarsa baiji dadin hakan ba dolensa ya hadiye sanin da yayi ta d'arashi a shekaru babu yanda ya iya mata.
Zaune ya iske Hajiya,mahaifiyar Siyama. Siyama tana kwance akan cinyarta. Ya k'arasa cikin ladabi ya durkusa yana gaisheta. Hajiya bata ko kalleshi ba ta amsa a ciki
"Lafiya."
Bai wani damu ba daman tun a baya Hajiya ba son aurensa da Siyama takeyi ba,kwarai taso 'yarta da auren d'aya daga cikin yaran masu hannu da shunin dake rububinta. Saidai Allah Yafi gaban haka,aure kuma kaddararSa ce. Ko bayan haka ma soyayyarsa da Siyama da kuma karfin zumuncin dake tsakanin iyayensu maza bana wasa bane.
Jafar dakyar ya iya yin tambayarsa
"Yaya jikin nata?"
Kamar jira Rumaisa takeyi,tayi saurin cafewa
"Bakinka baiji kunyar tambayar...."
"Kiyimin shiru,baki ganin a inda muke ne?"
Maganar Hajiya tasa Rumaisa hadiye sauran zancen tana mai kwafa. Kafin waninsu ya samu damar cewa wani abu,wani ma'aikacin asibitin ya fito daga dakin da suke fuskanta,suka maida hankali gareshi yayinda ya mik'owa Rumaisa takarda
"Ga result saiku mik'awa Doctor."
Tayi godiya,fuu ta wuce,Hajiya na biye da ita rike da hannun Siyama. Jafar baiyi k'asa a gwuiwa ba ya mara musu baya saboda yasan rashin binsu ma wata matsalar ce. Tausayin Siyama duk yabi ya rufeshi,har lokacin tunanin abunda ya faru gareta yakeyi saidai bai iya tsinkayar komai ba. Bayan likita ta kammala duba result ta d'ago tana murmushi tace
"Na tayaku murna She's pregnant."
Dam! Tamkar an soki kirjin Jafar,jin da yayi jiri yana son kwasarsa ne ya sanya babu shiri ya zube kan kujera. Allah shaida ba'a bakin cikin samun ciki na sunnah amma shi kam yaji. Yana son Siyama,yana son haihuwa saidai hankalinsa yayi mugun tashi jin cewar ciki ne da ita. Yanzun ma ya aka k'are da kazantar ta balle kuma har a samu rabon d'a? Ai fa saidai Allah Ya sassauta.
"Jafar bakaji abunda akace bane?"
Rumaisa wacce tun furucin likita ta zubo masa na mujiya domin jin abunda zaice ta katse tunaninsa. Ya d'ago kansa da sauri yana washe baki wanda ba don Allah bane,
"Naji Anti,farin ciki ne ya hanani magana."
Sai kuma ya tuno da Hajiya a wajen. Doctor ta dubesu bayan kammala rubuce rubucenta
"Oh wannan ne mijin nata?"
Har lokacin bai rufe bakinsa ba
"Eh nine."
Ta gyada kai tana murmushi
"Congrats."
"Thank you."
Ta miko musu file
"Sai a siya mata wadannan magunguna. Sannan itama ta dunga kula da kanta sosai. Ta kiyaye k'aidar shan magani. Allah Ya raba lafiya."
Sukayi godiya suka fito. Ya saci kallon Siyama,murmushita sakar mishi har baisan lokacin daya maida martani ba da nasa murmushin wanda ke had'uwa da zuciyarsa su k'ara masa wani d'aci. Yakai dubansa ga Rumaisa
"Anti kawo a amso magungunan."
Ta mik'a mishi su kuma sukayi waje.
Ya kammala ya fito ya iskesu cikin motar Rumaisa,magana sukeyi amma zuwansa ne yasa su yin shiru har saida yakai ga tsarguwa.
Ya mik'awa Rumaisa magungunan,ta karb'a a wulakance.
"Jafar."
Da sauri ya russuna
"Na'am Hajiya."
"Inaso nasan irin zaman da kakeyi da Siyama,nayi mamakin yanda muka je gidan da niyyar ziyartarta saidai muka isketa kwance cikin amai,gaba dayanta kaca kaca. Wane irin zama ne da har matarka bata da lafiya tun safe amma ace har ka iya sanya k'afa...."
"A'a fa Hajiya,wallahi bai sani..."
Cikin zafin nama Anti rumaisa ta kaiwa bakin Siyama bugu. A fusace Hajiya tace
"Shashashar banza kawai,ana nema mata 'yancinta 'yar iskar yarinya tak'i ganewa. Don ubanki inace ke da bakinki kika sanar damu tun bai fita ba kike a wannan yanayin? Shine salon ki maidamu yan iska kike shirin k'aryatawa?"
Gama maganar Hajiya,ta maida dubanta ga Jafar wanda haushi ya isheshi,yanda yakejin zuciyarsa inda ace ba mahaifiya take ga Siyama ba, da babu abunda zai hanashi barin wajen.
"Kaga Jafar,ba ni daka raina ba,ko Alhaji mahaifi ga siyaman da kake tak'ama shine jinin Alhaji Rilwan(mahaifinsa.),bazai yarda da wulakanci ba a aure. Don haka tun wuri ka chanja takunka don muddin ka cigaba da tafiya haka zan fito fili na nuna maka dagaske nake bani kaunar aurenka da Siyama. Ja motar mu tafi."
Ta k'arashe tana mayar da dubanta ga Rumaisa. Rumaisa da zuciyarta tayi fes da wannan wankin da Jafar yasha a wajen Hajiyarsu,ta gyara zama ta rufe k'ofa. Mik'ewa yayi har lokacin bai samu damar cewa uffan ba,yana duban yanda Siyama tayi wani rau rau da ido,Rumaisa ta figi motar ta saitata suka fice daga asibitin.
Ransa ya b'aci ba kad'an ba,wai me Hajiya da Rumaisa suke nufi dashi ne? Yasan Hajiya tun farko bata kaunar aurenshi da Siyama wannan kad'ai ya isa ya janyo mishi tsana a wajenta. Toh ita waccan uwar shishshigin baisan layin da zai ajiyeta ba,ko ita d'inma tana bayan Hajiyar ne,oho.
Cikin fusata Jafar ya bar asibitin bai dire ko'ina ba sai k'ofar gidan mahaifinsa.
Barka da kwana..!