Kakan Adam A. Zango ya rasu akan hanyar sa ta zuwa daurin auren Jarumin a kasar Kamaru
Mun samu labarin rasuwar, kakan fitaccen jarumin Dan wasan hausa na Kanny wood , Adam A. Zango mai suna Alhaji Shehu.
HAUSA TIMES ta samu cikakken bayanin cewa mamacin ya rasu ne a makon da ya gabata a filin jirgin sama na Lagos lokacinda yake shirin hawa jirgi zuwa jamhuriyar Kamaru domin shaida daurin auren jikan shi Adamu Zango,
Majiya mai tushe ta shaidawa HAUSA TIMES ta wayar tarho cewa, “margayin ya taka matakalar hawa jirgi sai kawai ya yanke jiki ya fadi”. Majiyar ta cigaba da cewa nan take aka dauke shi zuwa wani Asibiti a nan Lagos amma daga bisani ya rasu.
Alhaji Shehu mai kimanin shekaru 65 ya rasu ya bar mata Biyu da ‘ya’ ya da dama kuma tuni akayi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
Kafin rasuwarsa ya kasance kani ga kakakan jarumin wasan Hausa Adam A Zango wanda ya sake angwancewa da amaryarsa ta Biyu daga jamhuriyar Kamaru , Ummu Kulthum.
Title :
Kakan Adam A. Zango ya rasu akan hanyar sa ta zuwa daurin auren Jarumin a kasar Kamaru
Description : Kakan Adam A. Zango ya rasu akan hanyar sa ta zuwa daurin auren Jarumin a kasar Kamaru Mun samu labarin rasuwar, kakan fitaccen jarumin ...
Rating :
5