KAFIN KAYI BARCI
********************
'Dan uwa kafin barci ya daukeka, tsaya ka tambayi kanka : Shin ayyukan lada guda nawa ka aikata a yau??
* Shin ka samu dukkan sallolinka a Jam'i??
* Shin ka faranta ma iyayenka zuciyarsu ayau??
* Shin ka taimaki maraya ko Miskini ayau??
* Shin Kayi azkar din safe da yamma, da kuma sauran Zikirai ayau din nan??
* Shin Salati guda nawa kayi ma Ma'aikin Allah (saww) yau?
* Shin kayi Istigfari kuwa ayau??
* Hailala guda nawa kayi ayau??
* Shin ko zaka iya Qirgewa yawan zunubanka yau??
* Shin ayau ka runtse idanunka daga kallon Haram??
* Shin ayau ka hana harshenka yin magana cikin abinda bai shafeka ba.
* Shin ayau din nan sau nawa ka roki Allah ya baka aljannah?? Kuma sau nawa ka roki tsari daga shiga Wuta??
Kafin ka kwanta, tsaya kayi tunani akan kanka. Ka bama kanka amsa... Kayi ma kanka Hisabi. Kayi istigfari da hailala don neman yayewar matsaloli da bunkasar al'amari.
Mutukar zaka rika yiwa kanka Hisabi kullum, to in sha Allahu zaka samu Hisabi mai sauki aranar Lahira.
Title :
Kafin Kayi Barci
Description : KAFIN KAYI BARCI ******************** 'Dan uwa kafin barci ya daukeka, tsaya ka tambayi kanka : Shin ayyukan lada guda nawa ka aikat...
Rating :
5