Assalaamu Alaikum da fatan Mallam yana cikin Qoshin lfy tare da iyalai baki daya, bayan haka, Mallam tambaya ta ita ce don Allah Mallam yaya matsayin zanin gadon da maniyyi ko maziyyi ya taba lokacin da mutum yake saduwa da matarsa, shin za'a iya sake kwantawa akan zanin gadon koko sai an wanke shi? Assalaamu Alaikum.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Hukuncin ya rabu ne zuwa kashi biyu kamar haka:
Shi dai maziyyi dukkan Malaman Fiqhu sun yarda akan cewa Najasa ne. Don haka idan ya taba tufafi sai an wankeshi kafin ayi sallah da tufafin.
Shi kuwa Maniyyi, Mazhabinmu na Malikiyyah sun tafi akan cewa shima Najasa ne. Sai dai kuma malamai mafiya rinjaye sunce ba najasa bane. Kuma kowadanne suna da Hujjojin da suka dogara akai.
To indai maniyyi ya bushe ajikin Shimfidar, Idan aka kankareshi da farce shikenan za'a iya amfani da shimfidar. Amma koda maziyyin ne ko maniyyin in dai sun riga sun bushe za'a iya kwanciya akan shimfidar. babu wani aibu.
Sai dai kuma wankewar yana da amfani saboda muhimmancin tsafta.
Kuma zai yi kyau ma'aurata su rika shimfida wani zani ko Kyalle akan ainihin shimfidar dake kan gadon tun kafin su fara gabatar da komai.
WALLAHU A'ALAM.