Hukumar tsaro ta farin kaya a Nigeria wato DSS, ta fitar da wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ta Tony Opuiyo dangane da samamen da jami'an hukumar suka kai gidan Sambo Dasuki a ranar Alhamis.
Hukumar ta musanta wasu rahotanni da ke cewa jami'anta sun kai samame gidan tsohon mai bayar da shawara kan sha'anin tsaro na kasa, Kanar Sambo Dasuki, duk da wata kotu ta ce a bashi Fasfo dinsa don ya fita waje yin jinya.
Sanarwar hukumar ta ce jami'anta sun kai samame gidan tsohon mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki ne saboda ya ki amsa gayyatar da wani kwamitin bicincike da gwamnati ta kafa ya yi masa, domin ya zo ya yi bayanin abinda ya sani game da wasu kudade Dala biliyan biyu da aka kashe wajen sayo makamai a tsohuwar gwamnatin da ta gabata.
Hukumar ta ce ba ta da zabi illa ta bi hanyar da doka ta tanada domin ganin lallai ya bayyana.
Sai dai a martanin da ya mayar, tsohon mai bai wa Shugaban Nigeriar shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki, ya musanta cewa ya taba samun wata wasikar gayyata da ke neman ya bayyana a gaban wani kwamiti binciken sayen makamai.
bbchausa
Title :
Dasuki ya ki amsa gayyatarmu — DSS
Description : Hukumar tsaro ta farin kaya a Nigeria wato DSS, ta fitar da wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ta Tony Opuiyo dangane da samamen da...
Rating :
5