Rundunar Hisba a garin Dutse, Jihar Jigawa ta kama wani jami’in dan sanda da take tuhumarsa da laifin yi wa wata yarinya mai shekara 13 ciki ba tare da aure ba.
dan sandan mai suna Bello, da yake amsa tambayoyin dogarawan hukumar ta Hisba, ya yi ikirari da bakinsa, ya kuma rubuta a rubuce cewar shi ne ya yi mata cikin tare da daukar alkawarin cewar zai dauki nauyin ciyar da ita har ta haife abin da yake jikinta, gami da alkawarin cewar bayan an yi suna zai aure ta, idan ta amince.
Shugaban Hukumar Hisba, Ustaz Aliyu Galamawa, ya tabbatar da labarin, inda ya ce yarinyar mai suna Sadiya Auwalu, mazauniyar Unguwar Yalwawa a garin Dutse; ta shaida masu cewa tana da ciki wata biyar kuma suna tare da Bello dan sanda, tsawon wata shida baya.
A baya, da take bayani a gaban jami’an na Hisba, ta ce ba wai Bello ne kawai ya san ta ’ya mace ba, akwai wasu mutane biyu da su ma sun yi lalata da ita bayan haduwar ta da shi, kimanin wata biyu zuwa uku baya. Ta ce cikin mutanen akwai Lawan Usman da Amadu Magini, dukansu masu shekara 35 zuwa shekara 45.
Bayan dukkansu sun hallara gaban ’yan Hisba, sun tabbatar da cewa suna cikin wadanda suka neme ta. Kwamandan ya kara da cewa sun hada kudi har Naira dubu 11, aka ba ta domin ta rika ciyar da kanta kafin su sake kawo wasu kudin har ta haihu.
Da take mayar da jawabi, Sadiya ta ce ita kam ba ta san iya adadin da ta sadu da Bello dan sanda ba. Ta ce shi ne wanda ya yi mata cikin amma sauran wadancan mutane da ta ambata, sun taka sawun barawo ne. Ta kara da cewa koda ta haihu ba za ta auri Bello ba saboda ba shi da kamun kai. Ta ce shi fasiki ne, don haka ita babu wanda za ta aura sai kamili, mai nagarata wanda zai kula da rayuwarta. “Manemin mata, marar kamun kai ba mutum ne da za ni aura ba,” inji Sadiya.
A Litinin da ta gabata ce, Kwamandan Hisba na Jihar Jigawa ya gabatar da su a gaban Kotu Shari’ar Musulunci da ke Dutse. Bayan ambata shari’ar, alkali ya dage sauraren batun nan da mako biyu masu zuwa.
Title :
Hisbah Ta Kama Wani Dan Sanda Da Yi Wa Budurwa Ciki
Description : Rundunar Hisba a garin Dutse, Jihar Jigawa ta kama wani jami’in dan sanda da take tuhumarsa da laifin yi wa wata yarinya mai shekara 13 ciki...
Rating :
5