BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Salatin Allah da amincinsa su tabbata ga Ma'abocin ceto mai girma aranar Mahashar, Shugabanmu Masoyinmu, Kakan Hasan da Husaini tare da dukkan Iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa masu albarka.
Kamar yadda kuka sani, wancan karon anan ZAUREN FIQHU mun kawo wani darasi na musamman dangane da bayani akan wasu hanyoyi guda 33 wadanda idan mutum yabi kowacce guda daya tare da ikhlasi zai samu shiga Aljannah in Allah yaso.
Yanzu kuma In sha Allahu zamu kawo hadisai Sahihai wadanda acikinsu Manzon Allah (saww) ya fadi wasu abubuwa masu sauki wadanda idan mutum ya aikatasu zai samu lada mai mutukar yawa.
Amma kafin muci gaba, ina Qara jan hankalin Jama'a cewa su tayamu addu'a akan wasu mutane marassa tsoron Allah wadanda kullum basu da aiki sai dai su rika kwafar rubutun Zauren Fiqhu suna Editing dinsa suna chusa abubuwa na son ransu. Wasu daga cikinsu ma har sukan sanya sunayensu ko kuma sunan shafinsu ajikin rubutun.
Suna nan da yawa akan facebook da whatsapp. Mun kama wasu daga cikinsu munyi musu nasiha sun dena, amma wasu har yanzu suna yi.
1. TASBEEHI : Tirmidhiy ya fitar da Hadisi daga Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa :
"DUK WANDA YACE 'SUBHANALLAHIL AZEEM WA BI HAMDIHI' ZA'A SHUKA MASA BISHIYAR DABINO ACIKIN GIDAN ALJANNAH".
2. KALMOMI BIYU : Hadisi daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra) daga Manzon Allah (saww) yace :
"KALMOMI GUDA BIYU SUNA DA SAUKI AKAN HARSHE, AMMA SUNA DA NAUYI AKAN MIZANI. KUMA ABABEN SO NE AWAJEN ALLAH MAI RAHAMA - SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI SUBHANALLAHIL AZEEM.
(Bukhariy da Muslim ne suka ruwaitoshi).
3. AT-TASBEEHUL MUDHA'IF : An karbo hadisin daga Uwar Muminai, Nana Juwairiyyah Bintul Harith (ra) tace : Manzon Allah (saww) ya fito daga wajenta alokacin da zai sallaci Sallar Asubah, alhali tana cikin wajen da take sallah adakinta.
Sannan ya dawo wajenta bayan Walaha (wato Hantsi) alhali tana nan zaune awajen. Sai yace mata :
"SHIN BAKI GUSHE DAGA KAN YANAYIN DA NA TAFI NA BARKI AKAI BA?" Sai tace "Eh".
Sai yace ''HAKIKA NI NA FADI WASU KALMOMI GUDA HUDU ABAYANKI, NA FADESU SAU SAU UKU.
DA ACHE ZA'A AUNASU DA DUKKAN ABINDA KIKA FADA AYAU DIN NAN GABA DAYA, DA SAI SUN RINJAYESU:
(GASU NAN) SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI 'ADADA KHALQIHEE, WA RIDHAA NAFSIHEE, WA ZINATA 'ARSHIHEE, WA MIDAADA KALIMAATIHI".
(Sahihu Muslim).
4. SADAQATUN JARIYATUN (SADAQAH MAI GUDANUWA KODA BAYAN RANKA): wannan ya kunshi abubuwa masu yawa kamar Gina Masallatai ko Makarantun Islamiyyah, ko Gina Gidan Marayu, ko Gina Rijiya, Ko kuma biyan kudaden karatun Likita ko Malamin addini, ko kuma Kulawa da tarbiyyar Qananan yara tare da dorasu bisa turba tagari (Koda ba yaranka bane).
Ko dasa bishiyoyi, ko gina asibitoci ko dakunan karatu (Libraries) na addini.
To wadannan abubuwan ladansu zai ci gaba da samunka koda kana cikin Qabarinka.
Hujjah ta anan shine hadisin nan shahararre wanda Maluman hadisi da dama sun ruwaitoshi. Yana nan acikin AL-JAMI'US SAGEER na Suyutiy. Manzon Allah (saww) yace :
"IDAN MUTUM YA MUTU, AIKINSA YA YANKE KENAN SAI DAI TA HANYOYI GUDA UKU :
a.) SADAQAH MAI GUDANUWA.
b.) KO ILIMI WANDA AKE AMFANA DASHI.
c.) KO KUMA 'DA (YARO) NAGARI WANDA ZAI RIKA YI MASA ADDU'A".
(Hadisi ne Sahihi).
5. KARANTA QUL-HUWALLAHU : Kowacce Qafa daya idan ka karanta, zaka samu ladan wanda ya karanta Hizifi 20 na Alqur'ani.
Hujjah anan ita ce Hadisi na 2,663 acikin Sahihul Jaami'i.
Manzon Allah (saww) yace : "SHIN YANZU 'DAYANKU ZAI KASA KARANTA SULUSIN ALQUR'ANI AKOWANNE DARE?
DOMIN KUWA DUK WANDA YA KARANTA "QUL-HUWALLAHU AHAD ALLAHUS SAMAD" ACIKIN WANI DARE, TO HAKIKA (KAMAR) YA KARANTA SULUSIN ALQUR'ANI NE ACIKIN DARENSA".
(Abinda ake nufi da Sulusi shine kashi daya cikin uku - ⅓)
6. SALLAR JUMA'A : Acikin kowanne takun Qafar da mutum yayi zuwa sallar Juma'a, zai samu ladan Azumin shekara guda da kuma Qiyamullailin ta.
Malamai suka ce Hatta duk Matar da take kwadaitar da Mijinta da kuma 'ya'yanta akan zuwa Sallar Juma'a da Wurwuri, ita ma zata samu irin wannan la dan cikakke kamar yadda Mijin nata da 'ya'yanta suka samu.
Hujjah anan ita ce Hadisin nan na 6405 Acikin Sahihul Jaami'i. Manzon Allah (saww) yana cewa:
"DUK WANDA YAYI WANKA RANAR JUMA'A, KUMA YAYI SAMMAKO YA TAFI MASALLACI A QAFA, BAI HAU ABIN HAWA BA, KUMA YA KUSANTO KUSA DA LIMAMIN. KUMA YA SAURARESHI, KUMA YAYI SHURU BAI YI SURUTU BA, TO AKAN KOWANNE TAKU GUDA DA YAYI TUN DAGA GIDANSA HAR ZUWA MASALLACI ZA'A BASHI LADAN AZUMIN SHEKARA GUDA TARE DA (LADAN) TSAIWAR DARARENTA".
7. YIN SALLAR ASUBAH DA KUMA ISHA'I ACIKIN JAM'I : Duk wanda ya sallaci wadannan salloli biyu acikin Jam'i, to Allah zai bashi ladan wanda ya kwana yana sallah.
Hujjah anan ita ce hadisin da Manzon Allah (saww) yake cewa: "DUK WANDA YA SALLACI ISHA'I ACIKIN JAM'I (LADANSA) KAMAR YA SALLACI RABIN DARE NE.
WANDA KUWA YA SALLACI SALLAR ISHA'I DA KUMA SALLAR ASUBAHI ACIKIN JAM'I KAMAR YA SALLACI DAREN NE (BAKI DAYA).
(Sahihul Jaami'i hadisi na 6342).
8. TAFIYA DOMIN YIN SALLAH ACIKIN JAM'I :
Manzon Allah (saww) yace : "DUK WANDA YA TAFI DA QAFARSA ZUWA GA SALLAR FARILLA ACIKIN JAM'I, TO (LADANSA) KAMAR AIKIN HAJJI NE.
WANDA KUMA YA TAKA DA QAFARSA ZUWA GA WATA SALLAR NAFILA (LADANSA) KAMAR NA UMRAH NE TA NAFILA".
(Sahihul Jaami'i hadisi na 6556).
Anan zamu tsaya da fatan Allah shi amfanar damu da abinda muka karanta. Kuma Zauren Fiqhu yana fatan kowa daga cikinmu zai yi kokarin aikata wadannan abubuwan domin samun wadannan garabasar.
Kuma muna Qara jan hankalin Masu Kwafar rubutun Zauren Fiqhu cewa suji tsoron Allah su dena chanza mana abinda muka rubuta. Kuma su dena cire sunan wajen da suka kwafo.
Yin haka ya zama cin amanar Ilimi. Duk mai yin haka ba zai samu abinda ake nema ba. Sai dai in ya tuba.
An gudanar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP -4) ranar laraba 25-11-2015
Title :
Hanyoyin 25 Masu Sauki Domin Samun Lada Mai Yawa
Description : BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Salatin Allah da amincinsa su tabbata ga Ma'abocin ceto mai girma aranar Mahashar, Shugabanmu Masoyinmu, Ka...
Rating :
5