1- Idan ka shiga gidan kace
Assalamualaikum' shaaidan zai bar
gidan!
2- Ka rika yawan bata labarai. Saboda Allah (S.w.t) ya sanar da mu
dan Adam yana son labari.
3- Ka zama mai yawan yabonta,
musamman a wajen da ake kusheta
ka nuna 6acin ranka.
4- Ka zama mai yawan bata kyaututtuka. Kyauta tana kara dankon soyayya.
5- Ka share wasu daga cikin kuskurenta.
Ka nuna baka ma san ta yi ba.
Kuma ka dauka a matsayin abinda ya
shude, karka ajiye shi a kwakwalwarka.
6- Ka nuna mata tausayawarka gareta a fili, musamman a lokacin da take
da juna biyu ko take jinin al'ada.
7- Kada ka daukaka abokanka fiye da
matarka. (lokuta da dama wasu mazan
suna fifita abokansu na karatu ko na
sana,a sama da matansu) 8- Ka nuna mata babu wata budurwa
dake gabanka sai ita, Ka nuna mata
kullum a matsayin sabuwa take a
gurinka.
9- Ka rika tunawa da ita a cikin addu'arka.
Hakan zai kara kauna tsakaninku. 10- Kada ka nuna mata ce wa kana yi
mata alfarma akan wani kyatayi da
kake mata, kamar siyan abinci,Saboda
daman hakkinta ne ka kawo mata,sannan
kasan ce wa abincin kawai kake kawowa
amma Allah shi ne mai ciyarwa. 11- Shaidan ne abokin gabarka ba
matarka ba,Lokuta da dama idan mata da
miji suka dan samu sa6ani har takai ana
maida martani cikin fushi,To katuna ba
daga ita bane shaaidan ne ke zugata,
Saboda shi yana mutukar son ayi saki. 12- Ka dauki abinci ka saka mata abaki.
Annabi (s.a.w) ya ce, "abincin ba cikinta
kadai zai shiga ba, zai huce har zuwa
zuciyarta."
13- Ka kasance mai yawan yi mata
murmushi/fara'a domin Manzo (s.a.w) ya ce: "Duk wanda ya nunawa matarsa
fara'arsa to dai-dai yake da yin sadaka."
14- Ka zama mai yawan neman
shawararta.
(wasu suna ce wa ba,a shawara da
mata). To ku sani ce wa manzo (s.a.w) ya kasance yana shawara da matansa.
15- Kar ka 6oye mata damuwar ka,
farin cikinka ko bakin cikinka.
Domin ita magani ce a tattare daka