Babban Maganin da zai hanaka yin Zina, shine:
1. tsayuwa abisa tafarkin Allah da gaskiya.
2. Cikakken Tsoron Allah a zuciya. Tare da kwadayin
samun Rahamarsa.
3. Kulawa da yin Sallah akan lokaci, kuma acikin Jam’I.
Tare da neman ilimin sanin Sallar.
4. Zikirin Allah safe da yamma tare da neman tsarinsa daga
Sharrin Shaitan ako yaushe.
5. Tuna girman Allah da kuma Kusancinsa gareka/gareki.
Yana tare dakai/dake alokacin da kuke aikata wannan
Kaba’irar
6.Tunowa da girman azabar da Allah ya tanadar ma
MAZINATA a lahira.
7. Tuno wa shaitan da kuma kaidinsa da yake Qullawa
domin hallakar da ‘Yan Adam.
8. Gujewa kadaituwa da duk wata Matar da ba
Muharramarka ba/ko Namijin da ba Muharraminki ba.
9. Kaucewa kalle-kallen fina-finan batsa. Ko kuma wakoki
da hotunan batsa.
10. Kaucewa abota ko Qawance da duk wani saurayi
Mazinaci ko budurwa Mazinaciya.
12. Addu’ar neman tsari daga munanan ayyuka, da
mummunan tunani.
“Allahumma inni a’uzu bika min Munkaratil Akhlaaqi wal
Af’aali wal Ahwa’I.”
11. Ka tuna cewar Wannan da zaka yi zinar da ita:
‘Yar wani ce.
Qanwar wani ce.
Diyar wani ce.
Watarana kuma zata zama Uwar wani.
To yadda kayi Zina da ita, kaima sai anyi Zina da Uwarka,
ko Qanwarka, ko Diyarka, ko ‘yar da ka haifa.
Da fatan Allah shi kiyayemu daga wannan mummunan aiki.
Title :
Hanyoyin 15 Da Zaka Bi Domin Gujewa Aikata Zinna
Description : Babban Maganin da zai hanaka yin Zina, shine: 1. tsayuwa abisa tafarkin Allah da gaskiya. 2. Cikakken Tsoron Allah a zuciya. Tare da kwada...
Rating :
5