AS-SALAMU ALAIKUM
Malam sannu da kokari Allah yakara maka himma da daukaka ya sama ayukan ka Albarka
Malam minene alfano hakurin zama da irin wannan mace da ka fada muna wato BALLAGAZAR MATA?
Mutum ne da ke da mata wacce take dauke da mafi yawanci halaye nan ta BALLAGAZAR MATA bata taba baiwa mijinta hakuri ko ta nema afuwa ga mijin ta ba ko neman sulhu ba in mijinta yayi magana tayi hushi tayi kuka ta nemi saki maimakon ta bada hakuri ko ta nemi gafara, kuma gasi Allah ya bata salihin miji domin mijinta yaro ne da yake da dotijontaka baya karya kuma abinda baida amfani bai dameshi ba.
Daga wani bawan Allah.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Yana daga cikin hanyoyin da Ubangiji yakan jarrabi bawansa Mumini, ya hadashi da mace marar biyayya. Watakil ta dalilin hakurin zama da ita din ne Allah zai rika kankare maka zunubanka, yana daukaka darajarka.
Shi yasa Manzon Allah (saww) bai gushe yana yi mana wasiyya game da hakurin zama da mata ba, har zuwa karshen rayuwarsa.
Yace mana Muyi hakurin zama dasu. Domin su an haliccesu ne daga Qashin Hakarkari. Yace idan zakaji dadi dssu, to kaji dadin dasu tare da wannan karkacewar tasu. Domin idan kace sai ka mikar dasu sai dai su karye. Wato idan kace sai sunyi maka komai yadda kake so, abun ba zai yiwu ba.
Don haka ni dai shawarar da zan baka ita ce kayi hakuri ka rike matarka. Watakil jahilci ne yake damunta. Don haka kayi gaggawar sanyata a Islamiyyar Matan aure mafi kusa daku.
Idan tana jin nasihohi daga Malamai mata watakik zata gyara wasu halayen nata. Allah ya sawwake.
WALLAHU A'ALAM.
Title :
Hakurin Zama Da Mace Mara Biyayya
Description : AS-SALAMU ALAIKUM Malam sannu da kokari Allah yakara maka himma da daukaka ya sama ayukan ka Albarka Malam minene alfano hakurin zama da i...
Rating :
5