Ba Wannan ne Lokaci na farko ba da Shugabanni
suke daukan alkawari Wajen kawo Karshen Cin
Hanci da Sha'anin Tsaro, Kowane Shugaba
yanabin wasu matakai domin ganin ya cimma
nasarar hakan, amma wasu kuma kan samu
nakasu Wajen Hanyoyin Cimma Nasarar, imma de
daga 6angarensu ko kuma daga Hukumomin da
nauyin hakan ke rataya akansu, Wannan ta sanya
madadin abubuwan sudinga raguwa kusan sede
ace Kullum kara karuwa sukeyi, Matsalar tsaro
tuni ta sanya Kasar cikin tsaka me wuya,
musamman awasu Sassan arewacin Kasar nan,
hakan ta sanya Kullum rayukan Al'umma na
Salwanta, koda banda balahirar Boko Haram
akwae fadace-fadace masu nasaba da Kabilanci
agaruruwa irinsu Jos, Nassarawa da Benue,
dawasu sassan yankin Kaduna, Wannan ta Sanya
abun yazama yayi kaka-gida a6angaren, idan na
kintata dede tun Lokacin Obasanjo har yanzu
bamu sami Karfin Tsaron damuke bukataba,
takowace fuska matsaloli dasuka shafi Siyasa da
Kabilanci na taka mahimmiyar rawa wajen kara
hura wutar rikicin, Matsalar Kabilanci Akasar nan
Kusan tana bada goyon baya wajen kasa kawo
karshen fitintinun, yayinda kowa ke kokarin kare
nasa koda ace nasan ne da lefi, wannan shine
babban kuskuren da Shugabannin Kabilu da
Shugabannin Addinai Suke tafkawa, aYayinda
sukuma daya 6angaren Kullum babban burinsu
asamu wanda basaso da laifi kodon su dinga
yayata hakan amatsayin kare nasu 6angaren.
Haka idan kadubi matsalar Cin Hanci da Rashawa
Kullum kara tashi yakeyi, anutse idan kayi tunani
shima zakaga Kabilanci yataka mahimmiyar rawa
wajen kara ha6akashi, duk Cancantar mutum idan
gaban wanda banasaba, misali ba Kabilarsaba ko
Addininsaba to anan zakaga zallar Wariyar launin
fata, karshe yahana wanda ba nasan ba wannan
dama, yakawo nasa koda bai Cancanci wannan
gurinba, inde ze bashi na gwamna masu gidan
rana(kudi)..
Misali amatsayina na Mailafiya dana taho daga
6angaren Arewa, inason Ci-gaban yankin
amatsayinsa na Yankina, amma kuma Kullum
abin Kallona shine menene makomar Kasata?
Babu kasar dazataci gaba batare data hade
kantaba , haka babu wata al'umma dazata cimma
kyawawan muradunta batare data Samu Ci-
gaban Kasa ta fuskar kawar da 6angaranci da
Kabilanci ba, Sannan babu Al'ummar Ko Kasar
dazata Samar da Kyawun Shugabanci wa
al'ummarta batare data Girmama 6angaren
SHARI'A ba, tsayar da DOKA da ODA inji Hausawa
shine karshen duk wani hargitsi da tashin-
tashina, duk wanda yataka dokar Kasa duk
Mulkinsa da Girmansa to Doka tahau Kansa koda
hakan na nufin karshen Mulkinsa ko Martabarsa,
kodaga wane Kabila ko Yanki yafito Doka itace
zata hukuntashi dede da Karantsayen dayayi
mata, Wannan shine kadai zai Kawo tarnaqin da
ake ciki wajen Kawo gyara Asha'anin Tsaro da
Cin Hanci da kar6ar Rashawa.
Lalle Yakamata dame girma Shugaba Buhari Ya
Gyara harkokin 6angaren Shari'a na Kasar nan,
tareda basu duk irin karfin dasuke bukata, dukda
Kasancewar itama 6angaren shari'ar cike take da
Kalubale da magudin shari'o'I, hakika naji dadin
dauko mutane irinsu Abubakar Malami SAN da
Femi Falana SAN da Shugaba Buhari yayi, hakika
mutane ne dasuka dade cikin Harkokin Shari'ar
Kasar nan, sunada wayewa tareda Sanin
makamar Hanyoyin daza'abi don Kawo gyara da
Sauyi Wajen harkokin Shari'a a Kasar nan, Femi
Falana Esq anyi masa SAN a 2012, Abubakar
Malami kuwa a 2008, hakika Wannan gogewar
kadai ta Isa sukai 6angaren Shari'a Tudun Mun
Tsira.
By
Sunusi Mailafiya
Title :
Gyara Bangaren Shari'a Zai Kawo Gyaran
Cin Hanci Da Tsaro.
Description : Ba Wannan ne Lokaci na farko ba da Shugabanni
suke daukan alkawari Wajen kawo Karshen Cin
Hanci da Sha'anin Tsaro, Kowane Shugaba
yanab...
Rating :
5