Gwamanonin jihohi 36 na Najeriya sun ce ba za su iya ci gaba da biyan mafi karancin albashi na Nairia 18,000 ga ma'aikatansu ba, saboda yanayin tabarbarewar tattalin arziki da kasar ta samu kanta a ciki.
A karshen wani taron da suka yi a ranar Alhamis a Abuja a karkashin inuwar kungiyar gwamnoni ta Najeriyar, gwamnonin sun ce faduwar darajar man fetur ta yi mummunan tasiri a kan kudin-shigar da suke samu.
Gwamnonin sun ce dawainiyar biyan mafi karancin albashin ba ta da yawa a lokacin da ake sayar da gangar mai kan dala 126, sabanin yanzu da ake sayar da ita kan dala 41.
Sun bukaci su gana da Shugaba Muhammadu Buhari domin tattaunawa kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Gwamnonin sun ce hanyar da kawai za a bi domin magance wannan hali na ka-ka-ni-ka-yi shi ne a mayar da hankali kan harkar noma da hakar ma'adinai.
Title :
Gwamnonin Najeriya Baza su Iya Biyan Albashi 18000
Description : Gwamanonin jihohi 36 na Najeriya sun ce ba za su iya ci gaba da biyan mafi karancin albashi na Nairia 18,000 ga ma'aikatansu ba, saboda ...
Rating :
5