Rahotanni daga Kano a arewacin Nigeria na cewa bam din ya tashi a cikin jerin gwanon mabiya Shi'a da ke tattaki daga garin Kano zuwa Zaria ya kashe mutane 21.
Lamarin dai ya faru ne a kauyen Dakasoye da ke gaba da Kura, kuma daya daga cikinsu, wanda ya shaida wa BBC cewa mutane ashirin da daya sun mutu, ya kuma ce mutane da dama sun jikkata.
Ya kara da cewa daruruwan mabiya Shi'a daga arewa maso gabas da yammacin kasar ne suka taru a Kano, inda daga nan suka nufi Zaria domin juyayin "Yaumul arba'un", wato kwanaki arba'in da kashe Hussain, jikan manzon Allah (SAW).
A cewarsa, an fara kama wani mutum da bam din da bai tashi ba, kuma ya ce su biyu ne ke dauke da bam din, jim kadan sai na biyun da ke dauke da bam ya yi gudu ya shiga cikin masu jerin gwanon, inda ya tashi bam din da ke jikinsa.
A cewar sa, sun dauki gawarwakin, sannan suka ci gaba da yin jerin gwanon zuwa Zaria.
Title :
Graphic Photos :Adadin Mutanen Da Su Ka Rasu A Hari Kano Ya Karu Zuwa 22
Description : Rahotanni daga Kano a arewacin Nigeria na cewa bam din ya tashi a cikin jerin gwanon mabiya Shi'a da ke tattaki daga garin Kano zuwa Zar...
Rating :
5