Hukumar hana almundahana ta kasa (Hukumar EFCC), ta fara bincike da amshe kaddarorin mutane na kusa da tsohuwar ministar Mai, Diezani Alison-Madueke.
Jaridar The Nation ta bayyana cewa an fara amshe masu Sarkokin Zinari, motocin su da kuma kudaden su. Sannan kuma hukumar EFCC ta samu hadin gwiwa da hukumar hana laififfuka ta Ingila.
Mutanen dai an takaita fitar su daga Najeriya. Sannan kuma hukumar EFCC na gudanar da gadi a gidajen su a Abuja da Legas tana jira hukumar Ingila ta kama Diezani da laifi domin suma su kai su kotu.
Wata majiya ta bayyana cewa: “Zamu yi amfani be da yadda akeyi a sauran kasashen duniya. A yanzu dai mun amshe masu kudaden su da motocin su.
“Kila ma Ingila za a kai su donin su fuskanci hukunci a can. Domin gabatar dasu a nan Najeriya zaya zama aiki 2.”
Diezani dai na fuskantar zargin rashawa daga hukumomin Ingila. A watan daya wuce ne aka kwantar da Ita a asibiti Kuma aka yi Mata aiki aka ciwon daji.
Title :
EFCC Ta Fara Bincikar Na Kusa Da Diezani
Description : Hukumar hana almundahana ta kasa (Hukumar EFCC), ta fara bincike da amshe kaddarorin mutane na kusa da tsohuwar ministar Mai, Diezani Alison...
Rating :
5