1) A daidai lokacin da yan'uwa da Iyalansa ke hallara domin shirin yi masa bikin nasararsa sai suka kare da zaman makoki da juyayin rashin sa.
2) A daidai lokacin da Matarsa ke shirin zamewa madaukakiya shugabar matan jihar gaba daya "First Lady" sai ta kare da zamewa a sahun zawarawan jihar (Bazawara).
3) A daidai lokacin da 'yayansa ke shirin zamewa madaukaka 'yayan mai girma Gwamna sai suka kare da zamewa marayu 'yayan margayi.
4) A daidai lokacin da duniya ke damarar taya su murna sai suka kare da yi masu ta'aziyya.
5) A daidai lokacin da yake shirin zama a katafaren gidan Gwamnati sai ya kare da zama a kushewar (kabari)
6) A daidai lokacin da yake shirin zama tare da jami'an tsaro masu yi masa hidima sai ya kare da zama da mala'iku masu yi masa tuhuma
7) A daidai lokacin da yake shirin tarbar cicirindon mutane sai ya zabi ganin wanda ya so a sanda ya so sai ya kare da zama shi kadai tilo da ayyukan sa sai yadda ubangijinsa ya so!
Allah ya jikan shi!!
Wannan Aya ce babba gare mu masu sauran numfashi. Mu daina fankama da hauma-hauma, mu koma ga ubangiji mu bi dokokin Shi sau da kafa.!!!
Allah yasa mu yi kyakyawan karshe!!!
Title :
Darussa Bakwai Game Da Rasuwar Dan Takarar Gwamnan Jihar Kogi
Description : 1) A daidai lokacin da yan'uwa da Iyalansa ke hallara domin shirin yi masa bikin nasararsa sai suka kare da zaman makoki da juyayin ras...
Rating :
5