Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani ga masu caccakar sa dangane da kalamansa na cewa Najeriya ta talauce, inda suka ce ya na razana masu sha’awar zuba hannayen jari a kasar.
Shugaban ya ce ‘yan kasuwar kasashen duniya na da labarin hakikanin halin da tattalin arzikin Neriya ke ciki.
Buhari ya kara da cewa, kalamansa game da tattalin arzikin Najeriya gasjiya ne kuma fadin gaskiyar ne zai sa ‘yan kasuwar su yi sha’awar zuwa Najeriya domin zuba hannayen jari da nufin taimaka wa kasar.
A nashi bangaren shugaban kungiyar gwamnoni ta Najeriya kuma gwamnan jihar Zamfara, Abdul Aziz Yari, ya goyi bayan Buhari, inda ya ce, kalaman shugaban ba za su sauya ra’ayin wanda ke da masaniya game da halin da Najeriya ke ciki ba dangane da sha’awarsa ta zuba hannayen jari.
To sai dai Alhaji Hussaini Jalo, kusa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya mayar wa da Buhari martini, inda ya ke cewa, ya kamata a matsayinka na dan kasa, ka kare martabar kasarka amma ba ka bata sunanta ba.
Title :
Buhari ya mayar da martani ga masu caccakar sa
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani ga masu caccakar sa dangane da kalamansa na cewa Najeriya ta talauce, inda suka ce ya...
Rating :
5