Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi ikirarin cewa Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari yana shirin dora kasar kan turbar mulkin kamar karya ta hanyar yin amfani da Ministan Shari’a na kasa, Abubakar Malami wajen tilastawa Hukumar Zabe Ta Kasa INEC bayyana sakamakon cewa zaben Jihar Kogi bai kammalu ba.
Fayose ya yi zargin cewa Buhari yana amfani da Ministan ne kawai a kokarinsa na yiwa Kundin Tsarin Mulkin Kasa da Kundin Dokar Zabe kwaskwarima, ta yadda zai mayar da Nijeriya kasa mai bin tafarkin Dimokradiyya karkashin jam’iyya guda.
A cikin jawabin da ya fitar ta hannun mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai, Lere Olayinka, Fayose ya ce za su yi amfani da dukkan karfin da suke da shi na shari’a domin kalubalantar hukuncin da Minista ya yanke kan zaben Kogi. A cewarsa, Babbar Kotun Kasa ce kadai take da ikon bayar da mafita game da zaben.
Ya kara da cewa, “INEC ta bayyanawa duniya matsayinta a yanzu na cewa ba hukuma ce mai zaman kanta ba, domin ta yi amfani da ra’ayin lauyan Shugaban Kasa wajen yanke hukunci, mutumin da a lokuta da dama ya sabawa shari’a, kuma kowa ya san dan APC ne, yana kuma bai wa jam’iyyar goyon baya a zaben na Kogi.
Gwamnan ya ce, “Shugaba Buhari da APC sun bi ta barauniyar hanya don cimma manufarsu ta yi wa Kundin Tsarin Mulki da kuma Dokar Zabe garambawul, kasancewar suna tsoron a sake sabon zabe tun da sun san irin kitumurmurar da suka kulla, yanzu kuma suna ganin idan aka sake zubeban kwarya, ba za su kai labari ba.
Ya ci gaba da cewa “Abin kunya ne a ce zabe na farko karkashin jagorancin sabon shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya zo da sa-toka-sa-katsi, inda ya ce magudin da ake shirin yi a zaben Kogi da batun sauyan dan takarar APC alamu ne dake nuni da cewa da ma can abin da Yakubu ya zo yi kenan, bai wa Shugaban Kasa da APC damar cin karensu babu babbaka.
Gwamnan ya nuna cewa, nuku-nukun da aka yi da labarin mutuwar dan takarar APC, Yarima Abubakar Audu, alamu ne da suka nuna irin shirin da APC ta yin na murde zabe. “Sun riga sun yi magudi, to mene ne dalilinsu tun farko na boye labarin mutuwar Audu? Mutumin da ya rasu tun sanyin safiyar Lahadi, amma aka boye, ba a fada ba sai bayan da INEC ta bayyana cewa zaben bai kammalu ba.
“A fahimtata, APC ta so a bayyana sakamakon sun lashe ne tukun, yadda za su fadi cewa dan takarar mataimaki ne zai maye gurbinsa. Amma hakarsu ba ta cimma ba ruwa ba, shi ya sa suka sake bullowa ta wani gefen.”
A karshe ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tashi tsaye domin yaki da salon mulkin kamara karya da ya ce ana yi yanzu, “Idan masu fashin baki suka zuro ido irin wannan na ci gaba da faruwa, to tabbas za a wayi gari dimokradiyya da tsarin bin doka da oda ya zama tarihi a Nijeriya. Wanda a karshe zai shafi kowa da kowa har ya zamto an rasa tudun dafawa.” In ji shi.
Source Zuma Times
Title :
Buhari Na Neman Jefa Kasar Nan Cikin Mummunan Hali – Gwamnan Ekiti
Description : Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi ikirarin cewa Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari yana shirin dora kasar kan turbar mulkin kamar ka...
Rating :
5