Wannan wata budaddiyar shawara ce kuma gajeruwa, wata qila muqarrabansu na kusa su gani su gaya musu.
.
Haqiqa wannan gwamnatin mai ci yanzu ta yi sakwa-sakwa da lamarin shi'a, alhali tana sane da cewa qungiyar addini ce mai qoqarin mamaye qasa, ko dai a siyasance kamar yadda ta yi a Lebanon, Kuwait, Syria da Bahrain, ko da qarfin tuwo kamar yadda suka yi a Iraq da Yemen.
.
Wannan duk a kan hanyarsu ce ta mamaye duniya da mai da dukiyar kowa ta su, da zubar da jinin bayin Allah a banza, gami da wulaqanta addinin muslunci a gaban sauran manyan addinan
.
Ba shakka mun fuskanci bala'in Boko Haram, ko ma na ce har yanzu muna ciki ba mu tsallaka ba, in da za mu koma baya mu duba tarihi sosai za mu taras cewa Muhammad Yusuf shi ne maqagin Boko Haram, qasa kuwa ba za ta gaza gano inda ya rairayo wannan aqidar ba.
.
Har yau dinnan suna tafiya ne a kan sai qasa ta koma hannunsu, yadda za su sami damar miqa mu ga Iran, ina ba wa mahukunta shawara kan cewa:-
.
Su sake neman cikakken bayanai game da wannan aqida, da kuma abubuwan da suke hanqoron cin ma wa, saqo ne ga:-
Gwamnatin Tarayya
Gwannatin jahar Katsina
Gwamnatin jahar Sokoto
Gwamnatin jahar Kano
Gwamnatin jahar Kaduna
Gwamnatin jahar Bauchi
.
Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.
Written by Baban Manar Alqasim
Title :
Budaddiyar Shawara Ga Shugaban Kasa Da Gwamnonin Sa
Description : Wannan wata budaddiyar shawara ce kuma gajeruwa, wata qila muqarrabansu na kusa su gani su gaya musu. . Haqiqa wannan gwamnatin mai ci yan...
Rating :
5