Rahotanni daga Kano a arewacin Nigeria na cewa wani bam ya tashi a cikin jerin gwanon mabiya Shi'a da aka fi sani da 'yan uwa Musulmi da ke tattaki daga garin Kano zuwa Zaria.
Lamarin dai ya faru ne a kauyen Dakasoye da ke gaba da Kura, kuma ganau sun shaida wa BBC cewa, an fara kama wani da bam din da bai tashi ba, kuma ya ce su biyu ne ke dauke da bam din, jim kadan bayan hakan bam na biyu ya tashi.
Daya daga cikin ganau ya shaida wa BBC cewa ya ga mutane goma da suka jikkata, amma 'yan Shi'a sun hana kowa karasawa wajen da lamarin ya faru.
A cewar sa, sun dauki gawarwakin, sannan suka ci gaba da yin jerin gwanon zuwa Zaria.
Title :
Bom Ya Tashi Dan Yan Shi'a 15 A Kano
Description : Rahotanni daga Kano a arewacin Nigeria na cewa wani bam ya tashi a cikin jerin gwanon mabiya Shi'a da aka fi sani da 'yan uwa Musulm...
Rating :
5