A kalla mutane biyar sun rasu a wani hari da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai a arewacin Kamaru.
Wani jami'i ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, cewa wata mace 'yar kunar bakin wake ce ta tarwatsa kanta a gidan wani Mai gari inda ta hallaka shi tare da iyalansa baki daya.
An ruwaito cewa wasu 'yan kunar bakin waken uku su ma sun mutu a harin wanda ya faru a garin Fotokol kusa da kan iyaka da Najeriya.
Kungiyar Boko Haram a bana ta kai hare-hare da dama a kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Najeriya.
Bbchausa
Title :
Boko Haram Sun Kai Hari A Jihar Port Harcourt
Description : A kalla mutane biyar sun rasu a wani hari da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai a arewacin Kamaru. Wani jami'i ya shaidawa kamf...
Rating :
5