A Najeriya, wani dattijon dan siyasa Alhaji Tanko Yakasai ya soki yadda shugaban kasar Muhammadu Buhari ke tafiyar da al'amuran kasar.
A hirarsa da BBC, Alhaji Tanko Yakasai ya yi zargin cewa wasu manufofin da Shugaba Buhari ya bullo da su, da kuma salon yaki da cin hanci da matsalar tsaro, abubuwa ne da suke barin baya da kura.
Dattijon dan siyasar ya ce bai kamata ace an dauki kusan watanni biyar ba a nada ministoci ba, kuma hakan ya sa ayar tambayoyi ni dai a zuciyata, in ji Tanko Yakasai.
'Lokacin kamfe kowa ya san ban goyi bayansa ba kuma yanzu bayan ya hau na yi fatan ya yi nasara, domin idan ya yi nasara ina cikin wadanda za su ci moriya, idan kuma bai yi ba, ina cikin wadanda za su cutu' in ji dattijon dan siyasar
Alhaji Tanko Yakasai ya kuma ce ya na bai wa Shugaban Nigeria shawara ta kafar jarida kuma ya na fatan shugaba Buhari zai dau shawarwarinsa.
Sai dai fadar Shugaban Nigeria ta maida martani inda mai magana da yawun shugaban Nigeriya Malam Garba Shehu ya bayyana Alhaji Tanko Yakasai a daya daga cikin manya a Nigeria kuma ya ce ba za su yi jayayya da batu irin na dattijon dan siyasar ba.
Title :
Ban Taba Goyon Bayan Buhari Ba-Tanko Yakasai
Description : A Najeriya, wani dattijon dan siyasa Alhaji Tanko Yakasai ya soki yadda shugaban kasar Muhammadu Buhari ke tafiyar da al'amuran kasar. ...
Rating :
5