Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Najeriya sun ce a kall bama-bamai biyu ne suka tashi a kasuwar wayoyin hannu da ke farm centre a birnin.
Rahotannin dai sun ce wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake ne ake zargi da kai harin.
Wani dan kasuwar ya shaida wa wakilin BBC cewa ya hango matan sun wuce ta gaban shagonsa, jim kadan bayan hakan kuma sai ya ji karar fashewar bam.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Muhammd Musa Katsina ya ce rundunar 'yan sanda tana neman wadansu matan hudu da suma ake zarginsu da hannu a wannan hari.
Bam na farko ya fashe ne a waje yayin da dayan kuma ya fashe a cikin kasuwar.
Zuwa yanzu dai hukumomi sun ce mutane 15 ne suka mutu, da kuma 'yan kunar bakin waken, yayin da sama da mutane 50 kuma suka jikkata.
Tuni asibitocin jihar suka fara kokarin bai wa wadanda suka jikkata taimakon gaggawa.
Wannan dai shi ne karo na biyu da aka kai kasuwar wayoyi ta farm center.
Title :
Bama-Bamai Biyu Sun Tashi A Kasuwar Waya A Kano
Description : Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Najeriya sun ce a kall bama-bamai biyu ne suka tashi a kasuwar wayoyin hannu da ke farm centre a birni...
Rating :
5