Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa ba kowane minista bane za’a ba ma’aikatar da zaya jagoranta. Shugaba Muhammadu Buhari da kanshi ya bayyana haka a kasar Indiya lokacin da take taron. Ya bayyana cewa wasu ministocin sai dai su halarci taron zauren kasa na tsaro kawai.
Amma a wata fira da jaridar Daily Trust tayi da Garba Shehu, Shehu ya bayyana duka ministoci 36 zasu jagoranci ma’aikata.
Shehu ya bayyana cewa abunda shugaban kasa yake nufi shine ba kowane minista zaya samu cikakken iko ba. Ya bayyana cewa Buhari za yayi amfani da tsarin dake akwai na babban minista da karamin minista.
Yace: “Kun san akwai tsari a kasar nan na babban minista da karamin minista. A wata fira da akayi shugaban kasa ya bayyana cewa Najeriya zata yi sa’a idan za’a samu rabin ministoci 42 a gwamnatin shi.
Wata majiya ta bayyana cewa kila shugaban kasan ya rantsar da ministocin shi a ranar 4 ga watan Nuwamba. Femi Adesina ya bayyana cewa shugaban kasan zaya bayyana lokacin da zaya nada ministocin shi.
Title :
Ba Kowane Minista Za'a Ba Cikakkiyar Dama Ba
Description : Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa ba kowane minista bane za’a ba ma’aikatar da zaya jagoranta. Shugaba Muhammadu Buhari da kanshi ya bayya...
Rating :
5