Hukumar zabe ta Najeriya INEC, ta bai wa jam'iyyar APC damar gabatar da sabon dan takarar gwamna a jihar Kogi da ke araewacin Najeriya, sakamakon mutuwar dan takarar jam'iyyar Abubakar Audu a ranar Lahadi.
Kazalika, INEC ta sanya ranar 5 ga watan Disamba ta zamo ranar da za a kammala zaben jihar a mazabu 91.
A ranar Asabar ne al'ummar jihar suka kada kuri'unsu don zabar gwaninsu a zaben da ake gani mai zafi musanman tsakanin jam'iyyar mai mulki a jihar PDP da kuma APC.
Daga bisani hukumar INEC ta ce zaben bai kammalu sai an sake a wasu mazabun.