Ana ta dada samun nasarar kwatowa shanun da aka sace Arewacin Najeriya musamman bangaren Kano kamar yadda yake a wannan rahoto da wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana.
Alhaji Murtala Sulen Garo shine Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano kuma shugaban kwamitin mayar da shanu zuwa hannun masu su, ya bayyana yawan shanun da aka gano da wadanda aka mayar hannun masu su.
Shima Alhaji Tambari Yabo Mohammed mukaddashin Sufeton ‘yan sandan Najeriya mai kula da shiyyar Kano ya bayyana dalilan da suka gano na sace sacen shanun jama’a.
Ya zuwa yanzu dai Alhaji Murtala ya nuna cewa suna samun nasarar sada shanun da aka gano ga masu su bayan yin bincike da tabbatar da cewa ba a bawa wani kayan wani ba, su kuma barayin da suka shiga hannu ana mikasu ga hukuma don yi musu hukunci.
Title :
Ana Ta Samun Nasarar Kwato Shanun Sata a Kano
Description : Ana ta dada samun nasarar kwatowa shanun da aka sace Arewacin Najeriya musamman bangaren Kano kamar yadda yake a wannan rahoto da wakilinmu ...
Rating :
5