Masu jinyar ’yan uwansu a asibitin Waziri Shehu Gidado sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta duba matsalar rashin ruwa da wutar lantarki da ke addabar asibitin tun lokaci mai tsawo.
Wata wadda take jinyar ’yarta mai suna Rakiya Sulaiman ta shaida wa Aminiya cewa, matsalar rashin ruwa da rashin hasken wutar lantarki suna addabar al’umma don haka yana da kyau Gwamnatin Jihar Kano ta gaggauta kawo karshensu, ta yadda asibitin zai ci gaba da rike kambunsa.
Ta ce a kullum sai sun sayi ruwa leda biyu zuwa uku, wanda idan da akwai ruwa a asibitin za a samu afuwar dawainiyar sayen ruwa kamar yadda abin yake a yanzu.
Wakilinmu ya samu zagayawa cikin asibitin na Waziri Gidado da ke unguwar ’Yan Katako kuma ya samu ganawa da wani jami’in asibitin wanda kuma ya bukaci a sakaya sunansa. Ya bayyana cewa babu shakka asibitin yana fama da masalar rashin ruwa amma matsalar ta samo asali ne saboda tsaurin da kasar wurin take da shi kuma koda an haka rijiya ruwa ba ya samuwa wadatacce.
Title :
Ana Rashin Ruwa A Asibitin Kano
Description : Masu jinyar ’yan uwansu a asibitin Waziri Shehu Gidado sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta duba matsalar rashin ruwa da wutar lantarki...
Rating :
5