Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Nigeria na cewa wani dan gidan sarautar Kano ya janye karar da ya shigar da masarautar Kano da Sarki Malam Muhammadu Sanusi na biyu da kuma gwamnatin jihar kan wasu ayyukan rushe-rushe da ake yi a gidan sarautar ta Kano.
A makon da ya wuce ne Alhaji Salim Abubakar Bayero wanda kawu ne ga Sarki Muhammadu Sanusi II ya shigar da karar inda ya nemi kotu ta dakatar da aikace-aikancen gine-gine da ake yi a fadar Kano.
A cewarsa, matakin yin sabbin gine-gine zai janyo kawar da wuraren tarihi da suka shafe sama da shekaru 500 a gidan sarautar ta Kano.
A yanzu kotun ta amince da bukatar janye karar da masu korafi suka yi, sannan kuma bayanai na cewa za a warware matsalar a cikin gida.
A baya-baya nan masarautar Kano ta fuskanci wani rikicin na cikin gida inda aka tube babban dan marigayi Sarki, Ado Bayero, watau Lamido Ado Bayero daga matsayin Ciroman Kano bisa zargin rashin yin mubayi'a ga Sarki.
Title :
An yi sulhu a masarautar Kano
Description : Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Nigeria na cewa wani dan gidan sarautar Kano ya janye karar da ya shigar da masarautar Kano da Sarki Ma...
Rating :
5