An yi jana'izar dan takarar gwamnan jihar Kogi na jami'iyyar APC, Abubakar Audu a garin Ogbonicha.
Manyan 'yan jami'iyyar APC sun halarci jana'izar, cikinsu har da shugaban jamiyyar John Onyegun.
A ranar Lahadi ne aka sanar da rasuwar dan takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin jam'iyyar APC a zaben da aka gudanar ranar Asabar.
Lamarin dai ya rikita masu saka ido a kan harkar zabe a kasar, kasancewar ba a taba samun irin wannan yanayi na mutuwar dan takara kafin a bayyana sakamako ba.
Tuni dai masana shari'a a kasar suka fara muhawara a kan al'amarin siyasar jihar Kogi, wanda suke cewa ba a taba cin karo da irin sa ba, inda dan takara ya rasu kafin a kammala zabe.
Abubakar Audu ya rasu ne sakamakon rashin lafiyar da ba a fayyace ba.
Title :
An yi jana'izar Abubakar Audu
Description : An yi jana'izar dan takarar gwamnan jihar Kogi na jami'iyyar APC, Abubakar Audu a garin Ogbonicha. Manyan 'yan jami'iyyar A...
Rating :
5