Hukumomi a kasar Bangladesh, a yau lahadi sun zartas da hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a kan wasu ‘yan adawa biyu na kasar wadanda aka sama da aikata miyagun laifufuka a lokacin da kasar ke gwagwarmayar ballewa daga Pakistan a shekarun 1970.
Magoya bayan jam’iyya mai mulki a kasar sun gudanar da bukukuwa na farin ciki a game da rataye Ali Ahsan Mohammad Mujahid da kuma Salahuddin Quader Chowdury, lamarin da ya yi matukar tunzara magoya bayan ‘yan adawa.
Yanzu haka dai an baza dimbin jami’an tsaro a birnin Dhaka fadar gwmanatin kasar domin kasancewa a cikin shirin ko-ta-kwana.
Title :
An rataye 'yan adawa biyu a kasar Bangladesh
Description : Hukumomi a kasar Bangladesh, a yau lahadi sun zartas da hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a kan wasu ‘yan adawa biyu na kasar wadanda aka sam...
Rating :
5